Sarrafa Albarkatun Gona: Ridi (3)
A wannan makon ne zan kammala wannan makala ta sarrafa ridi domin sayarwa a kasuwanninmu na cikin gida da na kasashen ketare. Idan ba a manta ba na fara wannann kasida makonni biyu da suka wuce, inda a makalar farko na gabatar da harkar ridin, wato na yi bayani a kan shi kansa rddin, da […]
A wannan makon ne zan kammala wannan makala ta sarrafa ridi domin sayarwa a kasuwanninmu na cikin gida da na kasashen ketare. Idan ba a manta ba na fara wannann kasida makonni biyu da suka wuce, inda a makalar farko na gabatar da harkar ridin, wato na yi bayani a kan shi kansa rddin, da inda ake samunsa a cikin kasar nan da amfaninsa a matsayin abinci, da magunguna da kayan shafe-shafe. Na kuma yi bayani game da girman kasuwarsa a ciki da wajen kasar nan.
A makala ta biyu da na yi a makon jiya, na yi bayani game da ire-iren ridin da mu ke da su kashi uku , da kuma wurare da shiyyoyin da za a iya samun kowanne, da kuma amfanin kowanne iri daga cikinsu. Na kuma fara yin bayani a kan yadda za a surfe ridi domin tace man da ke cikinsa ko auna shi ya zuwa kasashen ketare.
A yau zan tashi daga kafofin surfa ridi. Na yi bayanin yadda ake surfa ridi da hannu a makon da ya gabata, na kuma yi tsokacin cewa farashin surfaffen ridi ya fi na ridin da ba a surfa ba a kasuwannin duniya. Kuma mafi yawancin masu sayen ridi na kasashen waje na bukatar sa a surfe. Ana surfa ridi da injin surfa shi, wanda hakan ya fi kyau ga mai saye. Kodayake injinan surfen ba su da yawa a kasar nan, yanzu sun fara samuwa, musamman ma a manyan birane da garuruwa da ake samun ridi, kamar su Kano da Fataskum da garin Doma a Jihar Nasarawa da Oturkpo a Jihar Biniwai da Malam Madori ta Jihar Jigawa; sai kuma Jihar Legas inda kamfanonin da ke sarrafa ridi domin yin kayayyakin masana’antu. dan kasuwa zai bincika a masana’antar kasuwanci ta jiharsa, ko kuma kungiyar ‘yan kasuwar ridi mafi kusa da shi.
Farashin tan din ridi a Najeriya na kamawa kimanin Naira dubu 50, ya danganta da lokacin da aka saye shi; farashin na kasa dubu 50 a kakarsa, yana kuma wuce haka idan ya taho karewa. Farashin ridi a kasuwannin kasashen duniya na kamawa daga Dalar Amurka dubu da 250 (kimanin Naira dubu dari biyu) a tan, ya zuwa Dala dubu da 500 (Naira dubu 250), ya danganta da kyawun ridin da kuma gyaran da ya samu.
Na yi bayanin cewa man ridi ya fi kowane man albarkatun gona tsada, kamar su gyada da na angurya da man ja, da dai sauran su. Ana sayar da tan din man ridi a kan dala dubu biyu da 500 (kimanin Naira dubu 300), shi kuwa man gyada bai fi Dalar Amurka dubu daya ba (kimanin Naira dubu 170), shi kuwa man angurya bai fi dala 700 ba (kimanin Naira dubu 100).
dan kasuwa na iya matse ridinsa ya sayar da shi a matsayin mai. Akwai hanyoyi biyu na tatse man ridi; Matsar Sanyi, wacce ake matse man ridi domin amfani da shi domin abinci, da kuma Matsar Zafi wacce ake yi domin yin sauran kayayyakin masana’antu. Kowace matsa na da irin injin yin ta. Ana samun man ridin da aka yi wa matsar sanyi da kanshinsa, sakamakon na matsar zafi.
dan kasuwa na iya aikawa da ridinsa ya zuwa kasuwannin kasashen waje ta hanyoyin da na yi bayani a baya. Yana kuma iya sayar da ridinsa ga manyan kamfanonin da ke sayar da shi a kasuwannin waje ko su ke sarrafa shi a masana’antu gida. Za a iya samun irin wadannan kamfanoni a manyan biranen kasar nan, musamman ma Kano da Legas. Ban ba dan kasuwa shawarar ya matse man ridinsa domin fita da shi kasuwannin waje ba, ida ba ko ya samu mai sayen da ya bukaci ya yi hakan ba.Ko yaya dan kasuwa ya sayar da ridinsa zai ga albarka, domin harkar tana da tsoka.