Sarrafa Albarkatun Gona: Tafarnuwa (2)
Na fara duba harkar saye da sayar da tafarnuwa a kasuwanninmu na gida da na waje, a makon da ya gabata, a cikin jerin makalun sarrafa albarkatun gona da na ke gabatar wa masu karatu a wannan filin. A makalar na yi bayanin mahimmancin tafarnuwa a matsayin a na daya daga cikin kayan abinci da […]

Na fara duba harkar saye da sayar da tafarnuwa a kasuwanninmu na gida da na waje, a makon da ya gabata, a cikin jerin makalun sarrafa albarkatun gona da na ke gabatar wa masu karatu a wannan filin. A makalar na yi bayanin mahimmancin tafarnuwa a matsayin a na daya daga cikin kayan abinci da magunguna da aka fi amfani da su gaba daya a duniya, inda na ce kusan kowane jinsi na duniya na amfani da tafarnuwa, musamman ma wadanda ke zaune a kasashen da ke cikin Hamada da makwabtansu, da kuma kasashe masu sanyi. Haka zalika mu ma a Najeriya, musamman ma a arewacin kasar nan, muna amfani da tafarnuwa wajen maganin cututtuka da sanyi ke haifarwa, da kuma kare jiki daga irin wadannan cututtuka. Wannan dimbin amfani na tafarnuwa ya sa jama’a ke bukatarta, ya kuma sa take da daraja kwarai a kasuwannin gida da na kasashen waje.
Na kuma yi bayanin yadda a kimiyyance masana ilmin magunguna a duniya suka hakikance suka kuma tabbatar da ingancin tafarnuwa a matsayin sinadarin da ke inganta lafiyar jikin dan Adam. Kadan daga cikin alfanun tafarnuwa ya hada da gyara zuciya da habaka garkuwar jiki da ba jiki kariya mai mahimmancin gaske daga cututtuka,tafarnuwa na kuma taimakawa kwarai da gaske wajen zagayawar jini a jikin mai amfani da ita, ta kuma fi kowane tsiro a duniya yawan wani sinadari a cikinta da ake kira ‘Germanium’da Turanci, wanda ke yaki da cutar daji (ko Cancer da Turanci). Tafarnuwa kuma na maganin tsiron jiki (ko tumor da Turanci), ta kuma saukar da hawan jini, ko hana jinin hawa, tana kuma daidaita yawan sigan da ke cikin jini ta kashe tsutsar ciki, ta kone man da ke jikin mutum da ka iya jawo masa hawan jini ko shanyewar jiki .
A wannan makon ne Zan yi bayani a kan iri-iren tafarnuwa da ake samu akkasashen duniya, musamman ma a gida Najeriya, tare da darajarsu, kuma in yi wa dan kusuwa mai niyyar shiga harkar saye da sayar da tafarnuwa bayanin yadda zai sarrafa ta domin samun alherin da ke cikin harkar. Ana samun tafarnuwa a Najeriya kala biyu, fara da ja (wacce ake kira Purple da Turanci). Kowacce tana da mahimmanci ga mai saye daga kasashen waje, wanda ya danganta da irin bukatar da yake da ita, domin a cikin biyun akwai sabanin yawan sinadaran da ke wadata jiki da bitamins na ajin ‘A’da na ajin ‘B’da na ajin’B2’ da na ajin ‘C’; da kuma sinadarin ‘Calcium’ da sa karfin kashi da hakora, da kuma sinadarin ‘Zinc’ da sauran sinadarai masu amfani a jiki.
Saboda haka, dan kasuwa da ke niyyar shiga wannan harkar ba zai sayi tafarnuwa ya ajiye ya saurari mai saye daga kasashen duniya ba, zai bari sai ya samu mai saye, inda shi mai sayen zai bayyana masa irin launin tafarnuwar da yake bukata, da yawanta da kuma yadda yake so a adana ta a aika masa da ita. A mafi yawantan lokuta, mai sayen tafarnuwa daga waje zai bayar da oda da lokacin kai masa tafarnuwar da ba zai kasa nisan mako shida ba. Idan dan kasawa ya samu wannan oda sai ya shiga neman busasshiyar tafarnuwa, ya kuma shiga gyaranta domin tabbatar da tsabtarta. Na sha maimaita bukatar gyaran kayayyakin gona da za sayar a kasashen duniya a cikin makalun da na yi a baya. Rashin gyara albarkatun gona kafin a fitar da su, da kuma bin ka’idar da mai saye ya bayar, na sa mai saye ya ki karbar kaya, ko kuma ya rage farashin da aka yi yarjejeniya da shi saboda rashin bin ka’idar ciniki daga mai sayarwa.
Zan tashi daga nan idan Allah Ya kai mu makon gobe |