Sarrafa Albarkatun Gona: Tafarnuwa (4)

Na samu sakonnin tambayoyi da neman karin bayani da yawa a kan wannan makala ta sarrafa tafarnuwa da sayar da ita a kasuwanninmu na gida da na waje. Wadannan bukatu na masu karatu sun tabo bangarori da yawa, wadanda mafi yawancinsu na yi bayaninsu a cikin zangonni uku na makalar da na yi, wadansu kuma […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Tafarnuwa (4)
Sarrafa Albarkatun Gona: Tafarnuwa (4)

Na samu sakonnin tambayoyi da neman karin bayani da yawa a kan wannan makala ta sarrafa tafarnuwa da sayar da ita a kasuwanninmu na gida da na waje. Wadannan bukatu na masu karatu sun tabo bangarori da yawa, wadanda mafi yawancinsu na yi bayaninsu a cikin zangonni uku na makalar da na yi, wadansu kuma karin bayani ake bukata, wadanda dukkaninsu idan aka nazarci  abubuwan da na gabatar a makonnin uku za a gamsu.To wadannan bukatu na masu karatu suna dayawa da ba zan iya lissafa su ba yanzu, ba kuma zan maimata ayyukan baya ba, amma a wannan makon zan duba kungiyoyin taimakon dan kasuwa domin harkar tafarnuwa a ciki da wajen kasar nan, domin na ga mafi yawancin sakonnin da ke bukatar karin bayani nan suka karkata.
    Kafin in fara wannan batu na kungiyoyin tallafi, ina son in ba dan kasuwa wadansu shawarwari guda biyu masu mahimmanci a kan sarrafa kayayyakin gona da sayar da su a kasuwannin kasashen waje. Shawara ta farko ita ce, dole dan kasuwa mai sha’awar irin wannan harka ya kasance mai neman bayani ne game da harkar, walau a kafofin labarai, musamman ma yanar gizo (internet) da kuma hukumomi da kungiyoyin da sana’ar ta shafa. Misali na san akwai kungiyar masu harkar karo da ta masu harkar ridi. Na kuma san sauran albarkatun gonar da ake sarrafawa ma ba za su rasa irin wadannan kungiyoyi ba. Su kuma wadannan kungiyoyi na kasancewa da alaka da hanyoyin samun irin wadannan kayayyakin gona a cikin sauki, da kuma alaka da masu sayen kayan a kasashen waje.
Wadansu hanyoyin samun bayanai masu mahimmanci a harka irin wannan sun hada da ma’aikatun gona da na kasuwanci da ke kowane babban birnin kasar nan. Akwai kuma cibiyoyin kasuwanci na jihohi da kuma cibiyoyin kasuwanci na kasa- da-kasa. dan kasuwa zai samu bayanan kasashe da ke da bukatar irin wadannan albarkatun gona daga wadannan wurare. Zai kuma samu ka’idoji na hukuma da na hukumomin kasa-da-kasa a kan irin harkokin da yake da sha’awar  yi. Wadannan kafafe kuma za su ba shi hasken farashin albarkatun gonar da zai harka a kai, a kasuwannin cikin gida da na waje.
    Shawara ta biyu ita ce, kasancewa zama dan kungiyar irin albarkatun gona da yake sha’awar harkarta; kungiyar masu harkar citta ko ta masu harkar tafarnuwa da sauransu. Haka kuma zai iya zama mai rijista a cibiyar kasuwanci ta jiharsu, ko kuma cibiyar kasuwancin kasa da kasa, misali cibiyar kasuwancin Najeriya da kasar Sin, ko ta Najerira da Amurka, da dai sauransu, ya danganta da kasar da dan kasuwa ke da niyyar yin harka da ‘yan kasuwarta. Alherin zama dan daya daga cikin wadannan cibiyoyi na da yawan da ba zan iya lasafta ba a wannan karon, mai yiwuwa a nan gaba.
    Mu dawo kan kungiyoyin tallafi. Na yi bayanin kungiyar hadin gwiwa ta ‘Edport Path’,  ta hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Amurka da Kanada da wadansu kasashen a gefe daya da kuma ‘yan kusuwar kasashen da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da ke sha’awar huldar tafarnuwa. Na yi bayanin cewa an kafa wannan kungiya ta hadin gwiwa domin samar wa ‘yan kasuwa masu bukatar kayayyaki irin haka daga kasashen Amurka da Kanada, da kuma inganta kasuwancin kayayyaki irin haka tsakanin wadannan kasashe da kasashe masu tasowa da ke samar da su. Na shawarci dan kasuwa a makalar makon jiya da ya nemi wannan kungiya a yanar gizo domin tambayoyi da karin bayanai a kan harkar tafarnuwa, walau a nan gida Najeriya ko a kasuwannin kasashen waje. To dan kasuwa ba wai zai tsaya a kan wannan kungiya ba, yana iya lalubar wadansu makamantanta a yanar gizo; abin da kawai zai yi shi ne ya yi cigiyar masu bayar da tallafi, misali a kan harkar tafarnuwa.