Sarrafa Albarkatun Gona: Yazawa (Kashu)
A wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai sarrafa Yazawa, abin da wadansu suka fi sani da shazawa ko kashu ko kashau (ko kuma cashew nut da Turanci). Wannan abun marmari dan itace ne mai kwallo a kansa da kuma zunbutu mai tsayi da taushi da ya kunshi ruwa mai zkki […]

A wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai sarrafa Yazawa, abin da wadansu suka fi sani da shazawa ko kashu ko kashau (ko kuma cashew nut da Turanci). Wannan abun marmari dan itace ne mai kwallo a kansa da kuma zunbutu mai tsayi da taushi da ya kunshi ruwa mai zkki da danko. Masu shan wannan abun marmari kan shanye wannan zunbutu mai zaki su yasar da kwallon da ke samansa. Wannan kwallo kuwa shi ne dan kasuwa zai bukata domin sarrafawa ya shigar a masana’antun gida da na kasashen ketare.
Ana samun yazawa a jihohin Arewa ta tsakiya da makwabtansu, da suka hada da Nasarawa da Kogi da Filato da Abuja da Neja da Kaduna da Binuwai da Kwara da Oyo da Anambara da Inugu. Ana samun itacen Yazawa a bayan gidajen mazauna wadannan jihohi da suka shuka domin samun abun cefane. Wadansu kuma su kan debi wani bangaren gonakinsu su shuka itacen domin samun kudi mai yawa a kakar ‘ya’yan itacen.
Sannan kuma akwai manya manoman yazawa da ke ware manyan gonaki domin noman wannan itaciya, inda za ka samu dubban gindin itaciyar a gona daya. Irin wadannan manoma na shuka wannan itaciya domin sarrafa ‘ya‘yanta su sayar wa masana’antun gida da na waje. Wadansu ma irin masu wadannan gonaki kan kasance suna da masana’antun da ke amfani da albarkatun ‘ya‘yan wannan itaciya. Katafaren noman yazawa ya fara inganta kimanin shekaru goma baya, yayin da hankalin Gwamnatin Tarayya ya karkata wajen habaka fitar da albarkatun gona zuwa kasashen waje domin samun kudaden shiga, maimakon dogara da man fetur a matsayin haja daya tilo.
Ita dai itaciyar yazawa nagge (ko saniya da Hausa) ce,‘jikinta babu na yarwa’. Ana amfani da ganyen itacen yazawa a masana’antu wajen yin kayan kanshin abubuwan ci da na sha (wato flabour da Turanci) da kuma magunguna. Akwai karo a jikin itaciyar yazawa, wanda ake tsagata ake diba, da masana’antu ke sarrafawa domin yin dankon gam. Haka kuma ana amfani da bawon itaciyar yazawa wajen yin jima da rini.
Shi kuwa kwallon yazawa na dauke da wani irin mai, mai matukar amfani ga msana’antu. Wannan mai na kunshe da sinadaran ‘Oleic acid’ da na ‘protein’. Masana’antu na amfani da wannan man wajen yin magunguna da maganin kwari da na kare katako daga gara da kuma sinadarin ‘resin’ na hada kayayyakin robobi.
Masana’antu na amfani da ita kanta yazawa wajen yin lamurjen sha, inda aka hakikance yazawa na dauke da sinadarin ‘bitamin C’ mai matukar mahimmanci ga jikin dan Adam, linki biyar fiye da wanda za a iya samu a cikin lemon zaki. Ana kuma yin magunguna daban-daban da tukar yazawa a masana’antu. Wannan dimbin amfani da ke tare da yazawa ya nuna bukatar da ake da ita a masana’antu gida da na waje. Akwai irin wadannan masana’antu da ke sarrafa albarkatun itacen yazawa, musamman ma kwarar da ke cikin kwallon yazawa, a kasar nan mafi yawansu a Legas suke. Ana bukatar albarkatun itaciyar yazawa a kasashen Turai da yawa, da kasar Amurka da wadansu kasashen Nahiyar Amurka da na Nahiyar Asiya.
Wadannan masana’antu masu sarrafa yazawa sun fara yawaita a Najeriya tun lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, yayin da tsarin gwamnatinsa na SAP ya waiwayi gonaki domin samun kayayyakin sarrafawa a masana’antunmu na gida, da kuma bukatar fitar da albarkatun gona zuwa kasashen ketare domin samun kudin shiga.
Zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai samu albarkatun itaciyar yazawa, musamman ma kwallon yazawa, ya sarrafa shi domin sayar wa masana’antun gida da na kasashen ketare idan Sarki Allah Ya kai mu makon gobe.
Ina yi wa masu karatun wannan shafi murnar shigowar sabuwar shekarar Nasariyya. Allah Ya ba mu alherin da ke cikinta ya kuma kade mana fitintinun da ke cikinta.