Sarrafa Albarkatun Gona: Yazawa (Kashu) (2)
Na fara wannan makala a kan yadda dan kasuwa zai sarrafa yazawa (ko shazawa ko kashu ko kashau, ya danganta da sunan da mai karatu ya santa da shi, ko cashew da Turanci) a makon jiya, inda na yi bayanin yadda take da kuma wuraren samunta. Na kuma yi bayanin amfaninta da kuma bukatar da […]
Na fara wannan makala a kan yadda dan kasuwa zai sarrafa yazawa (ko shazawa ko kashu ko kashau, ya danganta da sunan da mai karatu ya santa da shi, ko cashew da Turanci) a makon jiya, inda na yi bayanin yadda take da kuma wuraren samunta. Na kuma yi bayanin amfaninta da kuma bukatar da ake da ita a kasuwannin gida da na waje. Sai kuma na yi alkawarin a wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai samu albarkatun itaciyar yazawa, musamman ma kwallon na yazawa, da yadda zai sarrafa shi domin sayar wa masana’antun gida da na kasashen ketare.
Kamar yadda na yi bayani a baya, bukatar dan kasuwa ga wannan dan itace ita ce, kwallonsa da ake cirewa yayin shan zunbutun. Mai shan wannan abun marmari yana cire kwallon ya yar, saboda haka a wuraren da ake samun yazawa a kan samu yara da manya da ke yawo suna neman wadannan kwallaye da aka zubar, suna tarawa domin su sayar. Shi dai abun marmarin yazawa yana fadowa ne a kasa yayin da ya nuna, kuma saboda yalwar ruwa a inda yake, a kan samu ciyawa a kasan itaciyarsa a daidai lokacin da ya nuna. Manoman da suka shuka wannan itaciya domin samun abin cefane, wato kananan manoma, su kan sayar da abin marmarin itaciyar gaba daya. Su kuwa matsakaita da manyan manoma da suka shuka ta domin kwallon, suna cire kwallon su sayar da zumbutun da ake sha daban.
Saboda haka dan kasuwa na da kafa biyu na sayen kwallon yazawa; walau daga kananan masu tsinta daga inda aka sha yazawa su tara, ko daga manoman da su ka cire kwallon suka tara tun daga gonarsu. Wannan zabi na wurin sayen kwallon yazawa ya dogara da jarin dan kasuwa na yin wannan harka. Idan karamin jari gare shi, zai kasance sayen kwallon yazawa daga kananan dillalai, inda ya fi araha. Sai dai kuma a nan yana da gyara mai yawa, domin masu sayen hajjarsa na gida da na waje na da ka’idar tsaftar irin kayan da suke bukata fiye da masu sayen sauran albarkatun gona. Misali, mafi yawancin masu sayen kwallon yazawa na da ka’idar cewa sai an samu kwallo 200 a kowane kilo aya. Wadansu za su ce guda 170 ko 180 daga ciki su kasance lafiyayyu. Wannan ya danganta ga mai saye daga hannun dan kasuwa.
dan kasuwan da ke sayen wannan kaya daga kananan dillalai zai same su ne cirri-ciri, ba kamar yadda zai samu a hannun manyan dillalai ba ko a hannun matsakaita da manyan manoma ba. Farashin kayan ya fi tsada a hannun irin wadannan dillalai, sai dai an fi samun ingantattun kaya a gare su. Misali, manyan dillalan kwallon yazawa na zuwa gonakin kanana da matsakaitan manoma su saye abun marmarin, wani lokacin ma tun kafin ya nuna. Sai su cire kwallon su debe sannan su sayar da abun shan araha, saboda abin shan ba ya daraja baya kuma dadewa bai lalace ba in an cire kwallon.
Su kuwa manyan manoma su kan cire kwallon daban su kuma tare abun shan daban. Kamar yadda na yi bayani a kasidar baya, yawancin su sukan sarrafa wannan albarkatun gona ne a masana’antunsu, a matakin farko su sayar wa manyan masa’antun da za su mayar da hajjar abun anfanin al’umma a cikin Najeriya, ko kuma manoman su sayar wa irin wadannan masana’antu na kasashen ketare.
Zan yi bayanin matakan sarrafa kwallon yazawa da kuma ka’idar fitar da shi ya zuwa kasashen ketare da ake bukatarsa idan Allah Ya kai mu makon gobe.