Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale

A wannan makon zan fara bayani a kan yadda za a sarrafa zogale a matsayin daya daga  cikin albarkatun gona da za a iya sayarwa a kasuwanninmu na gida da na kasashen ketare. A yau a kasar nan zogale ba abin da za a yi wa mutum kwatance ba ne, musamman ma mutumin arewacin Najeriya. […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale
Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale

A wannan makon zan fara bayani a kan yadda za a sarrafa zogale a matsayin daya daga  cikin albarkatun gona da za a iya sayarwa a kasuwanninmu na gida da na kasashen ketare. A yau a kasar nan zogale ba abin da za a yi wa mutum kwatance ba ne, musamman ma mutumin arewacin Najeriya. A wadansu shekaru baya da ba su wuce goma zuwa ashirin ba, zogale wani ganye ne na wata itace mai matsakaicin tsawo da mutanen karkara ke tsinka da damina domin yin abinci, musamman ma abincin rana. A kan kwadanta zogale da kulikuli, ko kuma a yi dambun gero ko na garin kwaki da shi. Kuma a wancan lokacin a kan samu zogale ne a kan iyakokin gidajen karkara ko gonaki domin raba iyaka, saboda itaciyar zogale ba ta girma ko rassa masu girma, balle ta cika wuri. Mata kuma kan shuka shi a wani gefen gida domin tsinkar ganyensa da damina, tunda ba ya rassa manya domin a sha inuwarsa.
    Da ke nan, yanzu al ammura sun canza, zogale ya zama wata haja mai kawo wa mai ita dukiya. Saboda gane alherin da ke tattare da zogale, yanzu ya tashi daga matsayin shukar kan iyaka ya zuwa wani abu da manoma ke ware wa wadansu gonaki ko wadansu sassan gonakinsu domin dibar albarkatunsa su sayar su biya bukatunsu. Kuma maimakon a saurari zuwan damina domin dibar zogale, yanzu ana samunsa a kusan kowane lokaci na shekara, saboda ana shuka shi a fadamu.
    Zogale ya tashi daga cimakar talakawan Arewa yayin da likitoci suka tabbatar wa duniya cewa zogale na habaka garkuwar jiki, musamman ma ta mutanen da ciwon kanjamau ya karya. Suka kuma hakikance cewa yana maganin cutar daji da ta ciwon siga da kuma saukar da jinin da ya hau da kuma bayar da garkuwar ga shanyewar sassan jiki da magani ga wanda maciji ya sara da kumburin ciki da ciwon dasashi. Sannan kuma suka tabbatar da cewa zogale na inganta kwadayin jima’i da maganin kuraje da gyaran fata da lafiyar zuciya da hana farfadiya. Matan da suka haihu kuma na amfani da zogale wajen yawaita nonon da jariransu za su samu daga gare su. Zogale kuma na bayar da sinadaran da dan Adam ka rasa a abincinsa da suka hada da ‘bitamins’ da ‘protein’ da makamantansu.  
    Wannan fadakarwa ta zaburar da jama’a wajen nema da amfani da zogale, musamman ma ‘yan Najeriya ‘yan asalin kudancin kasar nan da a da ba su san abin da ake cewa zogale ba. A yau za ka ci karo da zogale a kasuwannin manyan garuruwa da biranenmu da manyan kantunan alfarma da kantunan mag
    Amfani da zogale kuma ya fadada, daga ganyensa ya zuwa ‘ya’yansa ya zuwa bawonsa da furansa da kuma saiwoyinsa. Za ka samu sarrafaffen zogale a wadannan kasuwanni a matsayin busasshensa, ko garinsa ko kuma busassun ‘ya’yansa da kuma a cikin siffar ganyen shayi na zamani. Masana’antu kuma na amfani da man da ake tatsa daga zogali wajen yin kayan abinci da turare da man shafawa da magungunan sha da na shafawa, musamman ma man gashi na mata. Ita kuwa tunkuzar da ta rage bayan tace man zogale, ana anfani da ita ne wajen yin takin zamani da sinadarin tace cututtuka daga ruwan sha da kuma tace gishiri daga cikin ruwan teku domin amfani da shi wajen sha da girke-girke.
    Wannan dimbin amfani da na lasafta sun nuna fadin kasuwar zogale da bukatun da ake da su wajen amfani da zogale.
Zan yi bayani kafofin samunsa da yadda za a sarrafa shi a kai kasuwanninmu na gida da na kasashen ketare, idan Sarki Allah Ya kai mu makon gobe.