Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale (2)
Zan yi bayani a kan kafofin samun zogale da yadda za a sarrafa shi a kai kasuwanninmu na cikin kasa da na ketare. A makon da ya gabata na yi bayani a kan irin alherin da ke tare da zogale wajen magance cututtuka daban-daban wadanda na zayyana a cikin makalar makon. Wannan ya sa zogale […]
Zan yi bayani a kan kafofin samun zogale da yadda za a sarrafa shi a kai kasuwanninmu na cikin kasa da na ketare. A makon da ya gabata na yi bayani a kan irin alherin da ke tare da zogale wajen magance cututtuka daban-daban wadanda na zayyana a cikin makalar makon. Wannan ya sa zogale ya samu karbuwa a kusan dukkanin sassan kasar nan da kasuwannun manyan kasashen duniya, musamman ma na nahiyar Turai da Amurka.
Wannan fadada da kasuwar zogale ta samu a duniya a cikin wannan karnin ya sa manoma da ‘yan kasuwa da masu masana’antu a wadansu kasashe da ake samun zogale suka yunkura wajen samar da zogale da sarrafa shi da kuma baza shi cikin kasuwannin duniya. A yau za ka iya sayen zogale a manya kantunan kasar nan, wanda aka sarrafa a kasashe kamar Indiya ko Malaysia ko Pakistan da sauransu. Irin wannan sarrafaffen zogalen na zuwa a mazuban da aka adana a cikin siga daban-daban, musamman ma a cikin sigar shayi.
Wannan ya sa dan kasuwan da zai shiga wannan harka zai kaddara cewa ba shi kadai ba ne cikin harkar, kuma zai yi tare da abokan sana’a na cikin gida da na waje. Kuma idan bai manta ba na yi bayanin yadda ake samun zogalen da aka sarrafa a kasuwanninmu na gida, to yanzu ga na wadansu kasashen ketare ya fara samuwa. Wannan ba zai karya gwiwar dan kasuwa mai niyyar shiga wannan harkar ba, domin wadanda ke cikinta ba su taba kashi daya daga cikin kashi 100 na kasuwar ba. Sai dai ya kasance yana sane da abokan fafatawa a cikin harkar, ya kuma san cewa inganta hajjarsa shi zai kasance sirrin nasararsa a cikin harka. Idan mai karatu bai manta ba, na yi makala a kan inganta kayayyakin da za a fitar da su kasashen ketare, a wani mako a baya kafin in fara makalar sarrafa albarkatun gona domin kasuwannin gida da na waje. A wannan makalar na yi bayanin ka’idoji da dokoki da mai niyyar fidda kayayyaki, musamman ma albarkatun gona, zuwa kasashen waje zai bi.
Za a iya samun zogale a dukkanin sassan arewacin kasar nan, musamman ma a jihaohin Arewa maso Yamma da kuma na Arewa maso Gabas. Babbar matsala a nan ita ce, zogalen da ake nomawa kalilan ne, duk da cewa ana samun karuwar manomansa a kusan kowace shekara, domin har gwamnatocin jihohi irinsu Kano da Kwara sun fara shiga noman zogale. Haka kuma ana samun shigar manyan manoma a cikin noman zogalen, amma duk da haka akwai karancinsa kwarai ga masu sarrafa shi. Wannan ya sa dan kasuwa mai bukatar ya samo zogale a karo daya ya sarrafa domin cim ma bukatarsa ta wadata kasuwar gida da ya tunkara, abu ne mai wuya, balle wanda zai auna ya zuwa kasuwannin ketare.
dan kasuwa da ke cikin wannan harka na da zabin ko ya nemi garuruwan da zai samu danye zogale a wurare ya saya ya sarrafa, ko kuma ya je kasuwannin kauye ya sayi busasshen zogale da aka kawo daga kauyuka ya saya. Wadansu da na sani masu irin wannan sana’a su kan yi amfani da kafofin biyu, wato su sayi danyen sannan kuma su sayi busassshen, domin su samu isasshen zogalen da za su iya sarrafawa domin isa kasuwar da su ke so su cim ma.
To kafin in yi bayanin sarrafa zogale domin kasuwannin gida da na ketare idan Allah Ya kai mu makon gobe, ina so dan kasuwa ya sani cewa danyen zogale ya fi kyau a gare shi ya samu domin sarrafawa. Sannan kuma ya san akwai matsaloli da yawa tare da sarrafa busasshen zogale da zai kai wadannan kasuwanni.
Zan bada shawara a kan wadansu dabaru na samun danyen zogalen ko ingantaccen busasshen idan Allah Ya kai mu makon gobe.