Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale (3)

A wannan makon ne zan yi bayanin sarrafa zogale domin kasuwannin gida da na ketare. Idan mai karatu bai manta ba a makon da ya gabata na shawarci dan kasuwa da cewa danyen zogale ya fi kyau a gare shi wajen sarrafawa. Na kuma sanar da shi a makalar cewa akwai matsaloli da yawa tare […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale (3)

A wannan makon ne zan yi bayanin sarrafa zogale domin kasuwannin gida da na ketare. Idan mai karatu bai manta ba a makon da ya gabata na shawarci dan kasuwa da cewa danyen zogale ya fi kyau a gare shi wajen sarrafawa. Na kuma sanar da shi a makalar cewa akwai matsaloli da yawa tare da sarrafa busasshen zogale da zai kai wadannan kasuwanni. Kuma saboda karancin zogale (musamman ma danye) a kasuwa domin sarrafawa, na yi alkawarin ba dan kasuwa shawarwari a kan wadansu dabaru na samun danyen zogalen ko ingantaccen busasshen a wannan makon.
 Sarrafaffen zogale na iya kasancewa a matsayin busasshen ganyen zogale da aka tsince wa kananan itacensa hakukuwan jikinsa da sauran tarkacen datti da ka iya kasancewa da shi. Ana kuma iya sarrafa zogale a matsayin garin busasshen zogale da kuma busassun ’ya’yan zogale ko kuma man busassun ’ya’yan zogalen. Ana kuma iya sarrafa hakukuwan rassan zogale da Turawa ke cewa ‘drumstid’ domin magunguna.
Babbar matsalar zogalen da za a sarrafa, idan aka dauke samurwarsa, ita ce ta kasa ko kura da sauran hakukuwa da ake iya samu a cikinsa. Wannan kasa ko kura ko hakukuwa na shiga cikin zogale yayin da aka shanya shi kafin a sarrafa, shi ya sa yake da kyau dan kasuwar da zai sarrafa zogale ya same shi danye ya busar da shi kafin ya sarrafa shi. An fi samun zogale a bushe a cikin manya buhuna a kasuwa domen sayen masu sarrafawa, sai dai kuma yawanci a kan samu irin wannan zogale da irin gurbacewar da na yi bayani a baya. Saboda rashin isasshen zogalen da za a sarrafa, masu wannan sana’a kan saye shi haka su je su tsabtace shi kafin su sarrafa shi.
Wani abu mafi wuya wajen tsabtace irin wannan busasshen zogale da aka saya a kasuwa shi ne fitar da kasa ko kura daga cikinsa. Wadansu na amfani da gishiri su sake wanke shi su shanya ya bushe. Dole dan kasuwa ya bi a sannu wajen wanke zogale domin fitar da kasar da ke cikinsa, domin yana iya wanke sinadarin da ake bukata a jikinsa, wannan zai sa a ki sayen zogalensa ya yi asara. Ana iya samun shawara daga ma’aikatun albarkatun kasa a jihohi domin shawara a kan yadda za a iya magance wannan matsala da ma shawarwari a kan hanyoyin sarrafa zogale baki daya.         
Idan kuma dan kasuwa ya samu danyen zogale domin sarrafawa, abin yi a gare shi shi ne ya shanya shi a wurin da kura ba za ta taso ta baibaye shi ba. dan kasuwa zai yi wa danyen zogalensa shimfida mai fadi, wadda za ta kasance akwai sarari tsakanin inda zogalen da ya shanya ya kare a kan shimfidar, da kuma karshen shimfidar. Wannan sararin zai kasance kamar inci 12 a kowane gefen shimfidar hudu. A kuma tabbatar cewa an sanya wani abu mai dan nauyi a kowane gefen shimfidar hudu saboda hana iska ta daga shimfidar.     
Ya fi kyau a shanya danyen zogalen da za a sarrafa a lokacin damina, musamman ma tsakiyar damina, lokacin da zogale ke cikin tashensa, domin babu kura da iska a lokacin in ba ko hadari ne ya taso ba. karshen damina zuwa kaka da lokacin rani aka fi samun iska da ka iya gurbata zogalen da aka shanya. To tunda ana samar da zogale daga noman rani a lokutan kaka da rani, wannan yanayin ma ba zai hana shanya zogalen ba domin busar da shi.  

    Zan yi bayanin yadda za a shanya zogale a irin wannan yanayi, sannan kuma in yi bayanin kafofin sarrafa busasshen zogalen domin kasuwanninmu na gida da na kasashen ketare idan Allah Ya kai mu makon gobe.