Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale (4)
A makalar makon jiya fara bayanin yadda dan kasuwa zai shanya danyen zogale domin sarrafa shi, inda na yi bayanai a kan yadda za a iya shanya ganyen zogale a lokacin damina ya bushe, na kuma yi alkawarin karin bayani a kan yadda za a shanya ganye zogalen da aka samu daga noman rani domin […]

A makalar makon jiya fara bayanin yadda dan kasuwa zai shanya danyen zogale domin sarrafa shi, inda na yi bayanai a kan yadda za a iya shanya ganyen zogale a lokacin damina ya bushe, na kuma yi alkawarin karin bayani a kan yadda za a shanya ganye zogalen da aka samu daga noman rani domin busar da shi da kaka. Na kuma ce zan yi bayanin kafofin sarrafa busasshen zogalen domin kasuwanninmu na gida da na kasashen ketare idan Allah Ya kai mu makon gobe.
dan kasuwa zai gina ko ya nemi dakin ajiya (wato store, da Turanci) mai girma domin shanyar zogale. Idan so samu ne, zai fi kyau a ce dan kasuwa ya gina irin wannan dakin ajiya, wanda tsayin katangunsa ba zai wuce kafadun mutum mai matsakaicin tsawo ba. Za a ci gaba da tsayin wannan ma’ajiyi da wayar shinge har ya zuwa matsayin rufi. Za a shanya zogale kamar yadda na yi bayani a makalar baya. Kuma ta kofofin wannan wayar da fadi da tsawon wannan dakin ajiya ne zogalen da aka shanya zai samu iska ya bushe. Sannan kuma daga ginin dakin ajiyar ya zuwa tsawon kafadar mutum mai matsakaicin tsawo zai hana kura taba zogalen. Domin wannan lokaci na bazara zuwa kaka lokaci ne na iska da ke dauke da kura.
dan kasuwa zai iya sayar da zogalen da ya busar a kasuwannin gida da na waje, ba tare da sarrafa shi fiye da wannan matsayi ba. Na yi bayanan wuraren da dan kasuwa zai iya sayar da busasshen zogale da sauran albarkatun da ake iya samu daga gare shi a kasuwanninmu na gida. Idan kuma dan kasuwa na iya samun zogalensa mai yawa, to yana iya sayar wa wadansu masana’antu da cibiyoyin bincike na cikin gida ko ya fitar da shi zuwa kasashen waje kamar yadda na yi bayani a makalun baya. Irin wadannan wurare sun hada da kamfanonin yin abincin dabbobi da na binciken lafiyar dabbobi, National beterinary Research Institute da ke Jos; da kamfanonin yin abinci da kayan shafa irin su United African Company (UAC) da Grand Cereal da dai makamantansu.
Idan kuma dan kasuwa na da isasshen jari, zai iya sarrafa zogalensa da ya busar ya zuwa ganyen shayi ko lamurje, ko kuma man girki ko na shafawa. Ana kuma iya yin abincin dabbobi da zogalen. dan kasuwa na iya samun karin bayanin yadda za a iya sarrafa zogale ya zuwa wadannan abubuwa da na lasafta, daga Cibiyar Bincike da Habaka kayayyakin Masana’antu ta kasa da ke unguwar Maitama a Abuja (wato Raw Material Research and Debelopment Institute).
Injin yin ganyen shayi karami, wanda zai iya yin ganyen shayi kimanin dubu 10 a yini daya zai kai kimamin Naira miliyan bakwai. Wannan inji zai nika ya tankace ganyen zogale ya maida shi gari mai laushi ya dura a cikin kananan mazuban gayen shayi na takarda mai laushi. dan kasuwa zai zuba wadanna mazuban gayen shayi a kwalayen da ya sa aka yi masa dauke da suna da adireshin kamfaninsa. A bisa al’adar masu wannan harkar a nan kasar, ana zuba ganyen shayi 10 ko 20 ko 25 a kwali, saboda haka zabi ya rage ga dan kasuwa ya zabi daya daga cikin tsarin guda uku. Idan dan kasuwa ya koma kan kasidun baya zai ga inda na yi bayanai a kan tsara abubuwan da aka sarrafa a masana’antu domin jan hankalin mai saye.
Idan kuma dan kasuwa ba shi da isasshen jari, zai iya sayar da busasshen zogalensa a matsayin ganye ko tankadadden gari da kuma ‘ya’yan zogalen. dan kasuwar da zai yi garin zogale zai kasance ya nika ganyen zogalen sosai ya yi laushi, sannan ya samu rariya da za ta tankade garin sosai. Domin cin nasarar wannan, dan kasuwa na iya sayen rariyar masana’antu da ake kira ‘industrial siebe’ da Turanci.
Na samu korafe-korafe daga masu karatu da suka ce na yi alkawarin yin bayanin yadda za a iya samun zogale da yawa, amma ban yi bayani a makalar baya ba. To zan yi wannan bayani, in kuma kara a kan sarrafa zogale, musamman ma ya zuwa lamurje idan Allah Ya kai mu makon gobe.