Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale (6)

Zan fara da cika alkawarin da na dauka a makon jiya na bayanin yadda dan kasuwa zai iya samun zogale mai yawa domin sarrafawa ya sayar a kasuwannin gida da na waje. Na samu korafe-korafe daga masu karatu da suka ce na yi alkawarin yin bayanin yadda za a iya samun zogalen da yawa, amma […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Zogale (6)

PIC.3.SHOPPERS AT THE YELWAN TUDU MARKET IN BAUCHI ON SUNDAY (22/12/13).

‘Yan kasuwa masu sayar da gwanjon kaya a kasuwar Yelwan Tudu da ke Bauchi a jajibirin Kirsimati Zan fara da cika alkawarin da na dauka a makon jiya na bayanin yadda dan kasuwa zai iya samun zogale mai yawa domin sarrafawa ya sayar a kasuwannin gida da na waje. Na samu korafe-korafe daga masu karatu da suka ce na yi alkawarin yin bayanin yadda za a iya samun zogalen da yawa, amma ban yi bayani a makalar baya ba, shi ne na yi alkawari a makalar makon jiya zan yi bayani a wannan makon. Zan kuma yi karin bayani a kan sarrafa zogale, musamman ma ya zuwa lamurje, kamar yadda na alkarwanta a makon na jiya.
    Game da samun wadataccen zogale domin sarrafawa ya kai kasuwa tunda akwai karancinsa a kasuwance, dan kasuwa na iya nazartar manoman zogale mafi kusa da shi, ko kuma manoman da yake shirin sayen zogalen da suke nomawa, domin basu jari su yi noman ya saya da kakar zogalen. Wannan tsohon sirri ne na masu sayen kayayyakin albarkatun gona. Masu wannan sana’a sun dade suna amfani da wannan tun lokacin Turawa. Su kan ba da kudi ga manoman gyada da na auduga da na karo da na bagaruwa da makamantansu tun damina. Ana yin wannan bisa yarjejeniyar manomi zai sayar da albarkatun gonarsa ga dan kasuwar da ya ba shi jarin da ya yi wannan noma.
    Ba manomi kudi na bunkasa nomansa, a samu albarkatun gona masu yawa, ya kuma ja hankalin wanda ba ya noma wannan abu da ake bukata ya samu karfin gwiwar noma shi daga lamunin da ya samu. Na karanta a wata jarida cewa akwai kungiyar manoman zogale ta jihohin Arewa da ke ba manoma irin zogale da za su shuka, su kuma ba su aron kudi domin su sayar musu da zogalen da suka shuka a farashi mai rangwame. Wata shawara ga dan kasuwa mai sha’awar wannan harka ita ce ya shiga kasar Nijar domin sayen zogalensa. Zogalen na samuwa fiye da nan Najeriya kuma a farashin da bai kai na nan ba. Kuma idan dan kasuwa zai iya tuna mukalar da na yi a wannan filin a kan cinikayya da kasashe makwabtanmu, albarkatun gona na cikin kayayyakin da aka amince a yi shiga da ficensu ba tare da haraji ba a kasashen Yammacin Afrika, wacce kasar Nijar na ciki.               
    Idan mai karatu na biye da ni zai iya tunawa cewa a makon jiya na yi bayanin yadda dan kasuwa zai iya busar da ganyen zogale ya sayar da shi a matsayin busasshen zogale, ko ya nika shi ya tankade ya sayar da shi a matsayin garin zogale. Na kuma yi bayanin yadda dan kasuwa zai iya mayar da busasshen zogalensa ya zuwa ganyen shayi. Yin lamurjen zogale a mtsayin abin sha bai bambanta da yin lamurjen lemo da na citta da na abarbaba da makamantansu da na taba yin bayani a kansu ba a farkon wannan shekarar. Kamar yadda na yi bayani a wannan makala, za a iya yin lamurjen zogale da inji mai saukin kudi, ko kuma da hannu. Babban abin kiyayewa shi ne tsabtar wurin da tsabtar kayan aiki da ta ma’aikatan wurin. Sai kuma rijista da hukumomi, musamman ma Hukumar kula da Abinci da Magunguna da kayan shafe-shafe (NAFDAC).
dan kasuwa zai kuma kiyaye da ka’idojin mazubi da kiyasin ruwar lamurjensa kafin a sha shi, kamar yadda na bada shawara a waccan makala.Sannan kuma kafin ya fara lamurjensa, ya zama dole ya nemi shawarar kwararru daga Ma’aikatar masana’antu ta jiha ko ta Tarayya, ko kuma Hukumar Inganta kayayyakin masana’antu (Raw Material Research and Debelopment Institute) da ke Abuja, ko cibiyoyin binciken abinci na gwamnati ko masu zaman kansu.