Sassan jikin mutum sun fado daga sama a kasar Saudiyya
Sassan jikin mutum sun fado daga sama a kasar Saudiyya, a birnin Jeddah, ranar Lahadin da ta gabata, inda jami’an ’yan sanda suka bayyana cewa ta yiwu sassan jikin wani ne da ya makale a cikin tayar jirgin sama.“’Yan sanda sun samu kira ta wayar tarho da karfe biyu da rabi na rana, daga wani […]
Sassan jikin mutum sun fado daga sama a kasar Saudiyya, a birnin Jeddah, ranar Lahadin da ta gabata, inda jami’an ’yan sanda suka bayyana cewa ta yiwu sassan jikin wani ne da ya makale a cikin tayar jirgin sama.
“’Yan sanda sun samu kira ta wayar tarho da karfe biyu da rabi na rana, daga wani wanda al’amarin ya auku a gabansa, inda ya ce sassan jikin dan adam sun fado daga sama a unguwar Mushrefa,” kamar yadda mai magana da yawun ’yan sanda, Nawaf bin Naser al-Bouk ya bayyana.
Da farko dai an yi zaton ko sassan jikin sun fado ne a lokacin da jirgi ke kokarin sauka,” a cewar al-Bouk, inda ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.
A yunkurin mutane na son tsallaka kan iyakar kasashe, wasu suka fakaici idon jami’an tsaro, a filayen jirgin sama da ba a tsaurara matakan tsaro, su lallaba su shige cikin tayar jirgi da ke rike da giyar sauka. Mafi yawansu sanyi ne ke daskarar da su har su mutu da zarar jirgin ya kai koli, amma wasu kan rayu.