Satar doya ta sa an yi masa zindir a Abuja

Karin an biyu da aka kama shi yana satar doya a gonar wani dattijo da ke ƙauyen ke nan

Satar doya ta sa an yi masa zindir a Abuja

Wata kasuwar doya

Al’ummar gari sun tuɓe wani mutum haihuwar uwarsa saboda kama shi yana satar doya a wata gona a Yankin Babban Birnin Tarayya.

An yi wa mutumin wannan ɗanyen hukunci ne bayan an kama shi a karo na biyu a gonar da ke yankin Kango a Ƙaramar Hukumar Kuje.

Wani mazaunin yankin, Bamaiyi Joshua, ya ce a yammacin ranar Litinin ne aka kama ɓarawon dayan a gonar wani dattijo mai suna Ishaya.

Ya ce a kwanakin baya Dattijo  Ishaya ya taɓa kama mutumin yana tona doya daga gonar, amma mutumin ya ba shi haƙurui da cewa yunwa ce ta sa shi aikata hakan, shi kuma ya yafe masa.

Bamai yi ta ce, “Ranar Litinin ɗin nan kuma mutumin ya sake dawowa gonar da buhu yana satar doya da masara.

“Amma ya yi rashin sa’a, wani manoma ya gan shi ya sanar da mai gonar.

“Aka je aka kama shi aka kai shi cikin gari, inda mutane suka ce da wa Allah Ya haɗa su, in ba shi ba? Suka tuɓe shi haihuwar uwarsa.

“Kafin ’yan banga su zo su tafi da shi, mutane sun riga sun lakaɗa mishi duka sun yi masa tsirara.”

Ƙoƙarin Wakikinmu na jin ta bakin kakakin ’yan sanda ta Abuja, SP Josephine Adeh, game da lamarin bai yi nasara ba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos