Satar fasaha ce matasalata —mawaki Abu Eliza
Wani matashi da ke waka da yaren Nufanci mai suna Abubakar Tadou da ke zaune a Legas ya ce satar fasaha da wadansu bata gari suke yi wa wakokinsa ne matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya.Mawakin dan asalin Jihar Kwara, wanda ake yi wa lakabi da Abu Eliza ya yi furucin ne yayin […]
Wani matashi da ke waka da yaren Nufanci mai suna Abubakar Tadou da ke zaune a Legas ya ce satar fasaha da wadansu bata gari suke yi wa wakokinsa ne matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya.
Mawakin dan asalin Jihar Kwara, wanda ake yi wa lakabi da Abu Eliza ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Eliza ya ce: “Za mu bata lokaci da kwakwalwarmu da tunaninmu mu tsara waka amma da mun fitar da ita sai masu satar fasaha ka ga tuni sun buga faifan sidi na wakokinmu suna sayarwa. Wani lokaci ma kafin wakar ta isa kasuwa sai ka ji tuni wasu sun buga ta suna sayarwa. Wani lokaci ma kasa da yadda muke sayarwa. Wannan al’amari yana damun mu.”
Ya ci gaba da cewa: “Sau da yawa ’yan kasuwa ne suke taimaka wa irin wadannan mutane masu satar fasaharmu domin mawaki zai yi waka ya buga ta da ya kai wa ’yan kasuwa sai su ki biyan sa kudinsa, wani lokaci ma sai su rika biyan ka kadan-kadan ta yadda ba za ka ci ribar komai ba. Ka ga wannan mugunta ce.”
Mawakin wanda yake jin Hausa da Turanci, ya bayyana cewa ya yi wakoki da dama a bangarori rayuwa iri-iri a harshen nufanci.
“Na yi wakoki da yawa don ba zan iya kirga yawansu ba a yanzu. Na yi wakar ‘Agibatujja’ da wakar ‘Eliza’ da ‘Kucilacici’ da wakar ‘Masoyi’ da sauransu amma ni gaskiya na fi son wakar ‘Eliza’ saboda da ita na yi fice kuma ta kunshi fadarkawa a kan wadanda suke boye yarensu da asalinsu saboda wata bukata da daban” Inji shi.