Satar fasaha: ‘Hukumar kare hakkin mallaka ba ta yi wa Kannywood komai ba’
Assalamu alaikum, ga ci gaban hirar da muka fara kawo muku da Alhaji Sani Abubukar Rainbow a makon jiya. Ya ce a dangane da satar fasaha Hukumar Kare Hakkin Mallaka ba ta tsinana wa Kannywood komai duk da yawan kudin da suke biyan hukumar. Ya bukaci jama’a su daina sayen fina-finai daga wurin masu satar […]
Assalamu alaikum, ga ci gaban hirar da muka fara kawo muku da Alhaji Sani Abubukar Rainbow a makon jiya. Ya ce a dangane da satar fasaha Hukumar Kare Hakkin Mallaka ba ta tsinana wa Kannywood komai duk da yawan kudin da suke biyan hukumar. Ya bukaci jama’a su daina sayen fina-finai daga wurin masu satar fasaha, idan ba haka ba kuwa Kannywood za ta durkushe.
Wadanne mataki kuka dauka?
Mun san wadanda suke satar fasaha, mun kai kararsu wurin hukuma, amma ba ta dauki matakin da ya dace ba, idan wannan masana’anta ta durkushe to za a yi babbar asara a Najeriya. A kwanakin baya an bayar da rahoton Najeriya ta fi kowace kasa a Afirka arziki, a kasar nan bayan harkar mai babu abin da ke samar da kudin shiga kamar harkar fim a Najeriya, wato Kannywood da kuma Nollywood. A wadannan masana’antu a wata biyu akan juya kudi fiye da Naira biliyan 2, amma a halin yanzu a cikin wata 2 ba a juya kudin da ya fi Naira miliyan dari 2, ka ga an samu ci baya. Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Najeriya (Nigerian Copyright Commission), ita take da hakkin kare mana hakkin fina-finanmu daga masu satar fasaha, mun ba Darakta-Janar din hukumar na kasa takardar korafi, mun bayar a ofishin hukumar da ke Kano, amma har yanzu kamar an shuka dusa. Kullum muka yi musu magana sai su rika neman kudi a wurinmu, don su yi mana aiki, akwai lokacin da suka fito da wata takarda mai dauke da yawan kudin da za su yi mana aiki a kowace jiha. Kada ka manta muna biyan kudi a kan kowane fim da muka yi a ofishin hukumar na kasa da kuma na Kano, don haka babu dalilin da sai mun ba su kudi kafin su yi mana aiki, mun nemi ganin Darakta Janar din amma abin ya gagara, wani lokacin mukan yi amfani da ’yan sanda idan muka kama su sai su dauko lauyoyi, inda a nan za a ce mana ’yan sanda ba su da hakkin kama masu satar fasaha face hukumar kare hakkin mallaka.
Yanzu ba mu rabu da wannan matsalar ba kuma sai ga shi wata kunno kai, wato fina-finan Indiya da ake yi musu fassara da Hausa, ya kamata a rika sayar da su da yaren Indiya ne, ba wai fassara da Hausa ba, kuma hakkin tabbatar da wannan ya rataya a kan hukumar kare hakkin mallaka ta kasar nan ne, akwai wannan dokar a kundin tsarin mulkin kasar nan. A yanzu masu kallo sun raja’a wajen kallon wadannan fina-finan saboda rashin kishin al’adunmu da kuma addininmu, kuma hukuma na gani ta kasa yin wani abu, duk da cewa hakan zai bata al’ada, kada ka manta a cikin kashi 5 cikin 100 na masu kallon fina-finan Indiya ne suke fahimta, sauran ba sa fahimtar hakikanin abin da suke koyarwa, yawancinsu suna kallon rawa da waka da kuma fada ne, sai aka ce yanzu ana fassara su da Hausa, don haka Hausawa za su dauki tarbiyyar da aka kitso ta daga can.
Hukuma ta kasa la’akari da jama’ar da suke cin abinci a masana’antar shirya fina-finai ba, a yanzu ko da an kai fina-finan Hausa da Turanci ba a saya, sai dai fina-finan Hausa-Indiya.
Ko kun san wadanda suke fassara fina-finan Indiya zuwa Hausa?
An san shagunan wadannan mutanen da suke yin wannan harkar, suna da shaguna a Kano da Jos da sauransu. Mun rubuta takardar korafi zuwa hukumar Kare Hakkin mallaka kusan wata shida ke nan, amma ba ta dauki wani mataki ba. Akwai lokacin da Gwamnati ta kira mu, inda muka gana da Ministar Kudi, Dokta Ngozi Okonjo-Iweala da Ministan Al’adu na kasa da kuma Darakta Janar din Hukumar Tace Fina-finai ta kasa, wato a lokacin Shugaba Jonathan Goodluck ya ware wa masu shirya fina-finai na kasa Naira biliyan 2, inda za a ba kowane mai kasuwancin fim Naira miliyan 50, masu shiryawa kuma miliyan 10, sannan za a kai wasu kasashen waje don su yi kwas a kan fim, mun yi zama a Legas, inda muka fada musu kalubalen da muke fuskanta, mun fada musu ba a ba mu kudi ba ne maganin matsalarmu ba, a’a, duk kudin da gwamnati ta ba mu tallafi ne, mun ce musu muna bukatar gwamnati ta yi mana yaki da satar fasaha ne, idan gwamnati ta yi mana haka, to mu za mu samar wa gwamnati kudin shiga, ba za mu jira kudin da za ta ba mu ba, a nan minister kudi ta ce za a tura masu satar fasaha zuwa EFCC, sannan za a hada kai da ’yan sanda da hukumar kare hakkin mallaka don yaki da masu satar fasaha. Ta yi alkawarin satar fasaha za ta zama tarihi a Najeriya, yau fiye da shekara daya ke nan, ba mu gani a kasa ba, an sa mun cika fom, mun bude asusun ajiye amma kamar an aiki bawa garinsu.
Bayan kun ji shiru, ko kun sake tuntubar wadanda al’amarin ya shafa don jin inda zance yake kwana da tashi?
Kullum sakonni suke turo mana ta imel akan ana shirye-shirye, duk da cewa ministar kudi ta fada mana a cikin wata uku za a ba mu kudin, za a kuma yi yaki da satar fasaha, duk da haka duk fim din da za mu kai kasuwa sai mun biya hukumar tace fina-finai ta kasa, sannan mu yi ta Kano, sannan mu biya kudin kare hakkin mallaka a Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Najeriya, amma babu abin da aka yi mana.
Tun da hukuma ta kasa daukar mataki, ko a kungiyance kun dauki wani mataki da kuke ganin zai haifar muku da da mai idanu?
Wannan wani al’amari ne ne laifi babba, don haka mutum ba ya iya daukar doka a hannunsa face hukuma. Kuma dokar kasa ta ce ga wadanda suke da hakkin daukar mataki idan an yi maka laifi, ka ga a matsayinmu na ’yan kasa masu biyayya ba za mu iya daukar doka a hannu ba.
Ko kana da kira ga masu kallo?
Kira gare su shi ne idan har suna so su rika ganin fina-finamu, to su daina sayen fina-finai daga wurin masu satar fasaha, idan ba haka ba kuwa za a wayi gari mun kasa fito da fina-finai, inda masu satar fasahar ma ba za su samu abin da za su sata ba, sannan ina rokon gwamnati ta magance mana matsalar satar fasaha kafin mu durkushe.