Satar jarrabawa sabon Allah ne
Satar jarrabawa ya zama ruwan dare a al’umma, ya zama al’ada kuma halin na neman zama addini. dalibai su rika tunanin ko ba su yi karatu ba za su iya hayewa! Ba tare da wani habbasa ba! A kan haka akan bi hanyoyi da dama a makarantu daban-daban ko dakunan rubuta jarrabawar! Hakan ya zama […]
Satar jarrabawa ya zama ruwan dare a al’umma, ya zama al’ada kuma halin na neman zama addini. dalibai su rika tunanin ko ba su yi karatu ba za su iya hayewa! Ba tare da wani habbasa ba! A kan haka akan bi hanyoyi da dama a makarantu daban-daban ko dakunan rubuta jarrabawar! Hakan ya zama wani aibu ko cuta ga tsarin ilimi, domin a kullum sai ka sami dalibai na fito da sabbin salon da za su saci jarrabawa, ban da cewa ana ba malamai da masu sa ido kudi don su kauda kai. Satar jarrabawa wani tsari ne da ‘yan makaranta ke cin jarrabawa ta wasu hanyoyi kafin a rubuta jarrabawar, a yayin da ake rubutawa ko bayan an rubuta, ta yadda za su yi nasara, ba tare da karatu ba!
Malamai kan kauda kai a aji, sai a yi satar son rai! Kowa ya saci abin da zai iya, duk da cewa wasu yaran da ka kalli takardar ka san sun duba littafi domin ba su tsaya a inda ya kamata su tsaya ba! kuma idan ka ce su fada da baki sai su yi shiru! Akwai salon da ya fi shahara na samun jarrabawar kafin a rubuta ta! Sannan a wasu makarantun kudin da ka shiga ko baka rubuta komai ba ka ci jarrabawar! domin makarantun kudin ke sayen jarrabawar a dunkule! Ban da shiga da ake yi da kananan littattafan nan, a dukunkune takarda, a rubuta ko zane hotunan a cinya ko damtse, ana shiga da kwalkuleta, ko wayar selula. Akwai salon wani ya rubuta wani jarrabawarsa, ko a biya malaman su daga kafa a yi sata son rai,
Satar jarrabawa na tasiri ga wanda yake yin ta, da farko zai dauki karya a matsayin dabi’a, kwange da kimshe, satar naman miya, yaudarar samari da miji, cutar iyaye, kuma satar jarrabawa daya take da sata a banki ko satar kudin gwamnati, domin duk wanda yake satar jarrabawa ba abin da zai sa ya ki satar dukiyar al’umma idan ya fara aiki, kasuwanci koda zaran dama ta samu!
Babbar illar ita ce malamai na hada baki da dalibai, musamman masu rubuta jarrabawar fita daga makarantar watau firamare, sekandare ko aji uku! A koyaushe malamai na iya ganewa idan an sace jarrabawa ko an yi ta yadda ya kamata, amma sai nuna ba damuwa! duk da illar dake ciki, sai dalibi ya shiga yunibasiti ya gane kurensa, ko ya gama jami’a a matsayin jaki. Duk da a jami’a akan sa ido sosai, akan kawo bakin malamai su gudanar da jarrabawa a yunubasiti, sannan dalibai basu da yawa a zama daya, amma wasu malamai da dalibai sun san hanyar!
Wata illa ita ce salon na hana wadanda suke karatu yin karatun domin zasu ga wadanda basu karatun na wuce su, a haka sai su ma su fara halin beran. Wani abin takaici shi ne wai a cikin irin wadannan daliban ake samun malamai da alkalai da ‘yan sanda da likitoci da kanikawa da teloli da manaja da gwamna da shugaban karamar hukuma da kansiloli da ‘yan kasuwa da marubuta,
Mawaka da ‘yan fim su ke bangar siyasa, su sace kuri’u, sune masu magudin zabe, irin wadannan mutane tun suna kuruciya suka iya yaudara, kamun kafar manyan mutane da bin malaman tsibbu don tabbatar da burinsu. Sannan satar jarrabawa yasa ba a ganin kimmar satifikate din Najeriya a kasashen waje, kai ko Nijar da Ghana an san halin daliban Najeriya balle kasashe irinsu Saudiyya ko Ingila ko Masar, wadanda wani lokacin sai dalibi ya koma sakandare kafin ya fara digiri, ko sai ka yi kalimatu-shada a gaban kowa don su tabbatar kai Musulmi ne, don rashin yadda!
Haka ya sa idan muka kalli dabi’ar, kar mu yi mamakin shugabanninmu na yanzu, sai mu yi tunanin wasu irin dalibai, malamai, ma’aikata da shugabanni za a samu a gobe a matsayin jagororin kasar nan? Bugu da kari satar jarrabawar nan da muke gani daya ne da sabawa Allah.
Satar jarrabawa ba maganar gargadi ba ne, dole a dauki mataki, a dakatar, a rufe makarantar ko a kwace lasisin. Duk da ana gane mutum wajen intabiyu ko kuma ya jin kunya a cikin mutane, musamman idan zai gabatar da taro ko kuma magana a bainar jama’a baki, inda alamar tambaya za ta rika yawo akan masu saurare! Sai ka iske mutum ya gama jami’a ba ya jin Turanci ko bai fahimci fanin da ya karanta ba!
dalibai sai su gama sekandare ko wasika ba su iya rubutawa ba da Turanci ko Larabci, wadanda suka iya rubuta wasikun soyayya da Hausa sune hazikai, don tsananin koma baya. Tabbas ana bukatar gwamnati ta kara kasafin a harkokin da suka shafi ilimi domin a halin yanzu duk jihohin da suke ikirarin cewa suna ba harkar ilimi muhimmanci sai ka iske sama da yara dari a aji daya!
Satar jarrabwa ba taimako ne ba ga malamai, dalibai, iyaye, makarantar, jihar ko kasar, illa ce babba ga al’umma.
Za a iya daukar matakai, kamar rage yawan yaran da za su rubuta jarrabawa a aji daya a lokaci daya zuwa talatin ta yadda malamin zai iya hangar duk abin da ake yi a ajin. Sannan a rika sa dalibai na kai jakukkunansu gaban aji, a fitar da littattafai a hana yawon takardu a kasa ko a iska kafin a fara jarrabawa, kuma a bincike kowa kafin ya zauna. A fara a lokaci daya a gama a lokaci daya, domin wajen kai ko karbar takardu dalibai kan hargitsa ajin. A rika shirya Taron kara wa juna sani (seminar) ko lacca don fadakar da malamai game da illar shedancin satar jarrabawa. Sannan malaman addini su yawaita yin wa’azi game da ha’inci ko zamba, domin duk daya ne da zuku a wani kaulin cin amana mai kai mutane ga azaba.
Dadin dadawa satar jarrabawa na kaskantar da darajar ilimin kasa, halin na bayana cewa ma’aikatar ilimi ta kasa ta yi sake, ana karatu mara inganci tare da ba dalibai sakamakon karya.
Daga karshe ya kamata a kawo karshen wannan illar kafin ta gama da al’umma, domin wannan halin ne ya sa dalibai suka zama ragwaye, ba su iya karatu ko sun yi kwakwalwar ba za ta dauka ba, su dai su yi sata!
Zan rufe da fatan Allah ya shirya manyan gobe. “Sai mu ji tsoron Allah a duk inda muke”
Buhari Daure +2347035986444 Muryar Talaka [email protected]