Satar kayan tallafi: An samu gawar mutane hudu a cikin dam 

An tsinci gawar mutum hudu da suka fada Dam din Laminga, domin gudun kada jami’an tsaro su cafke su saboda wawushe kaya da suka yi a gidan tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara. A makon jiya ne zauna-gari-banza suka shiga gidan Dogara da ke daura da Dam din Laminga a garin Jos, suka sace abubuwan […]

Satar kayan tallafi: An samu gawar mutane hudu a cikin dam 

An tsinci gawar mutum hudu da suka fada Dam din Laminga, domin gudun kada jami’an tsaro su cafke su saboda wawushe kaya da suka yi a gidan tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara.

A makon jiya ne zauna-gari-banza suka shiga gidan Dogara da ke daura da Dam din Laminga a garin Jos, suka sace abubuwan amfanin yau da kullum a gidan.

Kakakin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, Omini Bridget, ta tabbatar wa da wakilinmu cewa an kai gawarwakin mutanen da aka samu a Dam din na Laminga.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa gawarwakin guda takwas ne, an dauki wasu zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wanda suka rasun, sun tsere ne tare da fadawa dam din, domin guje wa fadawa hannun jami’an ’yan sanda.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa