Satar mutane ta sa manoma tserewa su bar gonakinsu a Taraba

Manoma suna kaurace wa gidajensu da gonakinsu saboda matsalar masu garkuwa da mutane a kananan hukumomin Ardo-Kola da Bali a Jihar Taraba

Satar mutane ta sa manoma tserewa su bar gonakinsu a Taraba

Wasu manoma a gona

Daruruwan manoma suna kaurace wa kauyukansu saboda matsalar masu garkuwa da mutane a kauyukan kananan hukumomin Ardo-Kola da Bali a Jihar Taraba.

Binciken wakilin Aminiya ya nuna cewa akasarin wadanda matsalar ta shafa sun bar gonakinsu ba tare da sun girbe amfanin na suka noma ba, zuwa garin Jalingo tare da iyalansu.

Kauyukan da ’yan bindigan suka addaba sun kai 12, inda suka sace mutane masu yawan gaske wadanda suka hada mata da yara kanana.

Wata mata mai suna Talatu Adamu ta shaida wa Aminiya cewa duk mazauna kauyensu mai suna a Bendo Naje sun yi kaura sun bar gidajensu da gonakinsu na masara da shinkafa da waken soya ba tare da sun girbe ba.

Wata majiya ta shaida wa wakilin Aminiya cewa sojoji da maharba sun yi arangama da ’yan bindiga a wasu yankuna da matsalar ta yi kamari inda suka yin nasarar hallaka wasu daga cikin bata-garin suka cafke wasu.

Shugaban Kungiyar Maharban Jihar Taraba, Malam Adamu ya tabbatar wa wa wakilin Aminiya cewa sun yi nasaran kama wasu ’yan bindigan a wata arangama da bangarorin suka yi.

Kakakin Birget din sojin Najeriya ta Shida da ke Jalingo, A. Oni ya ce zai bai wa wakilinmu cikakken bayani kan lamarin, amma har zuwa lokacin rubuta wannan labarin, hakan bai samu ba.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024