Satar mutane ta tilasta wa attajirai guje wa garuruwansu
Masu satar mutane suna yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa suna ci gaba da cin karansu ba babbaka a Jihar Taraba inda suke tilasta wa masu dukiya suna kaurace wa garuruwansu musamman a kananan hukumomi biyu na jihar don tsira da rayukansu. Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa fiye da masu […]

Masu satar mutane suna yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa suna ci gaba da cin karansu ba babbaka a Jihar Taraba inda suke tilasta wa masu dukiya suna kaurace wa garuruwansu musamman a kananan hukumomi biyu na jihar don tsira da rayukansu.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa fiye da masu dukiya 30, akasarinsu manyan ’yan kasuwa da manoma da makiyaya ne suka yi kaura daga garuruwansu a ’yan watanin da suka gabata, saboda yadda masu satar mutane ke cin karensu ba babbaka a kananan hukumomin Gassol da Bali.
Garuruwan da wannan matsalar satar mutanen ta fi kamari sun hada da garin Mutum- Biyu hedkwatar karamar Hukumar Gassol da garuruwan Abba da Tella da Sabon-Gida da dan Anacha da Chul duk a karamar Hukumar Gassol.
Sai kuma garuruwan Maihula da Garba Chede da sauran kauyuka da ke cikin lungunan karamar Hukumar Bali.
Binciken ya nuna cewa an samu matsalar satar mutane a wasu sassa na kananan hukumomin Donga da Gashaka amma matsalar ba ta yi kamarin da ta yi a kananan hukumomin Gassol da Bali ba.
Binciken ya nuna cewa daga bara zuwa bana, an sace sama da mutum 30, cikinsu har da mata da suka hada da mahaihfiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba na yanzu.
Bayanai sun nuna cewa ’yan fashin, sun karbi kudaden fansa daga ’yan uwa da iyalan wadanda suka sacen da suka kai kimanin Naira miliyan 100.
Kamar yadda binciken ya nuna ’yan ta’addan suna da manyan bindigogi kuma a kan manya babura da ake kira boksa suke daukar duk wanda suka sata.
Masu satar mutanen suna amfani da wasu manyan dazuka da suke yankin Bali da wasu sassa na yankin Gassol da Donga wajen boye wadanda suka yi garkuwa da su har zuwa lokacin da za a biya kudin da suka nema daga hannun ’yan uwa ko iyalan wadanda suka sace.
Binciken ya nuna cewa a karamar Hukumar Gassol an sace Alhaji Alhaji Shuwa wanda falken shanu ne kuma an biya Naira miliyan tara kafin a sako shi, sai Alhaji Jedo wani mai harkar man fetur da sufurin motoci, wanda aka biya Naira miliyan bakwai kafin sako shi, sai Alhaji Ibrahim Buhu wanda aka biya Naira miliyan bakwai.
Sauran sun hada da Alhaji Yusuf da matarsa wadanda aka biya Naira miliyan shida kafin a sako su, sai Alhaji Ibrahim Lili Wuro-Jam shi ma an biya Naira miliyan hudu sai Alhaji Sanusi da Alhaji Bello daga garin Abba wadanda aka ce an biya kudi masu yawan gaske kafin a sako su .
Saura su ne Alhaji Buba Gauri da Alhaji Nuhu Badija da Alhaji danmaliki da Alhaji Bagobiri Tella da Alhaji Isa, su ma ’yan uwansu sun biya kudi masu yawan gaske kafin a sako su
A garuruwan Maihula da Garba Chede da Bali da Suntai da Suntai Daji da Baruwa an sace sama da mutum 15 kuma sai da aka biya wadanda suka sace su miliyoyin Naira kafin su sako su.
Wakilinmu ya gano cewa dukan wadanda aka sace manyan manoma ne da ’yan kasuwa kuma ana zargin cewa akwai hannun wadansu na kusa da su wajen sace su.
Aminiya ta samu labarin cewa a ranar Litinin da ta gabata cikin dare an sace Sarkin Fawan dan Anacha, Alhaji Garba Umar kuma har zuwa hada wannan rahoto ba a ji duriyarsa ba, kuma masu satar mutanen sun umarci Dagacin Karal, Malam Haruna Karal, cewa ya ajiye musu Naira miliyan hudu a wani wuri za su zo su dauka, in kuma ya ki, to zai gamu da fushinsu.
Mafiya yawan mutanen da wakilinmu ya zanta da su kan wannan lamari sun nuna matukar damuwa tare da zargin hukumomi kan nuna rashin damuwa da yadda ake yawan sace jama’a a yankin.
Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Abubukar Maishanu ya ci akwai alamun cewa ana son a tarwatsa al’ummar yankin ne don cimma wata manufa. Ya ce in ka dubi wadanda ake sacewa kusan duk jama’a daya ce kuma ’yan kasuwa wadanda suke neman na kansu ba tare da sun dogara da gwamnati ba. Ya ce da wannan lamari na faruwa ne a wani yanki na jihar da tuni hukuma ta dauki mataki a kai, amma da yake a nan ne ba wanda ya damu.
Halin da muka shiga a hannun barayin mutane
Wani wanda aka sace mai suna Alhaji Dauda ya shaida wa wakilinmu cewa da misalin karfe 10:00 na dare ne wadansu mutane su goma dauke da manyan bindigogi a kan babura biyar suka kama shi suka shiga daji da shi.
Alhaji Dauda ya ce jim kadan da shiga daji da shi, sai suka rufe masa ido da wani kyalle kuma suka gargade shi da kada ya yi magana ko ihu domin idan ya yi haka za su kashe shi.
Ya ce kafin su dauke shi sun kwace wayar hannunsa, kuma sun raba dare sun tafiya a kan babura sai da misalin karfe hudu na dare suka isa wani wuri a tsakiyar daji. Ya kara da cewa da suka isa wurin sai aka kwance masa kyallen da aka rufe masa ido ya gan shi a gaban wani katon mutum yana kwance a wani dan karamin gado. Ya ce mutumin wanda ga dukan zato shi ne shugaban wadanda suka sato shi ya ce masa ya kwantar da hankalinsa kuma muddin ya hada kai da su ba za su cutar da shi ba. Ya ce can da dare sai babbansu ya ce in yana son ya koma gida da ransa zai biya Naira miliyan goma.
“Na fada wa masu garkuwa da ni cewa ba ni da wannan kudi amma mutumin ya daka min tsawa ya ce in rufe bakina in kuma na ki yanzu ya harbe ni. Duk da rokon da na yi cewa su rage kudin don ba ni da wannan kudi da suka nema sun ki yarda,” inji shi.
Alhaji Dauda ya ce daga nan ne suka kira matarsa da waya suka ba shi suka ce ya yi magana da ita. Da jin muryarsa sai matar ta fashe da kuka sai babban ya kwace wayar ya fada wa matarsa cewa in tana son mijinta ya dawo da ransa maza ta hada Naira miliyan 10 za su fada mata inda za ta ajiye kuma kada ta yarda ta fada wa wani jami’in tsaro.
A cewarsa bayan kwana biyu kudin ba su samu sai suka yi masa barazanar cewa za su kashe shi muddin aka kara kwana daya wannan kudi ba su samu ba. “Jin haka sai na roke su da su sake kiran matata don akwai maganar da nake so yi da ita,” inji shi.
Alhaji Dauda ya ce da kyar suka yarda suka rage kudin zuwa Naira miliyan biyar. Kuma Naira miliyan biyar din ma sai da aka sayar da amfanin gonarsa aka kuma ranto wasu kudin daga abokai da ’yan uwa sa’annan suka cika.
Ya ce bayan sun tabbatar cewa an kai kudin inda suka ce a ajiye, sai suka sake daure masa fuska suka dora shi a bayan babur suka kawo shi wani wuri inda daga bisani ’yan uwansa suka same shi. Ya ce bayan an kwance kyallen sai ya fahimci cewa inda aka ajiye shi bai da nisa da babban hanyar zuwa garinsu.
Shi ma wani babban manomi mai suna Alhaji Musa Maimasara ya shaida wa wakilinmu cewa sai da ya yi kwana bakwai a hannun wadanda suka sace shi a cikin wani daji yamma da Bali. Ya ce a wannan daji akwai masu aikata laifuffuka daban-daban da suka hada da masu sace mutane da ’yan fashi da makami da barayin shanu. Ya ce wadanda suka sace shi sun ba shi labarin duk abin da ya mallaka daga amfanin gona zuwa dabboninsa har ma da yawan motocin da yake da su.
Alhaji Maimasara ya ce wadanda suka sace shi sun nace cewa dole sai an ba su Naira miliyan 15 kafin su sake shi. A cewarsa da kyar suka amince suka karbi Naira miliyan goma kafin su sako shi.
Wata mijiya ta shaida wa wakilinmu cewa ana zargin akwai hadin baki a tsakanin wadansu na kusa da masu dukiyar da masu satar mutanen, ganin barayin mutanen suna da labarin duk harkokin kudi da ke gudana a wadannan garuruwa, saboda haka sun san irin mutanen da suke sacewa don a ba su kudin fansa.
A wata hira da wakilinmu ya yi da Shugaban karamar Hukumar Gassol, Alhaji Yahuza Ya’u ya nuna damuwarsa kan matsalar yawan sace jama’a da ake yi a karamar hukumar.
Ya ce matsalar ta kai inda ta kai domin duk wani dan kasuwa ko babban manomi da ke yankin hankalinsa ba a kwance yake ba.
Alhaji Yahuza Ya’u ya kara da cewa muddin jami’an tsaro ba su dauki matakin dakile wannan lamari ba, to za a ruguza harkokin kasuwanci da noma, kuma kowa ya kama gabansa ya bar yankin.
Shugaban ya ce akwai albarkatun noma da kiwo da kasuwanci da suka sa jama’a daga sassan kasar nan suke shiga yankin. Ya ce a duk lokaci ana harkokin arziki a yankin wadanda suka hada saye da sayar da kayan amfanin gona da cinikin dabbobi da kifi kuma ga kasuwancin itacen Madarid wanda ake kai wa kasar China.
Ya ce dole ne a dauki matakin magance wannan matsala kafin ta watsa al’ummar yanki baki daya.
Shugaban karamar Hukumar Donga, Mista Nashagu Namusa ya bayyana cewa ’yan sintiri da jam’an tsaro sun samu nasarar shawo kan wannan lamari ta hanyar kama wadansu daga cikin masu satar mutanen a yankinsa. Ya ce an shiga daji an tarwatsa gungun masu satar mutane kuma a halin yanzu an samu saukin satar jama’a a yankin na Donga.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Dabid Masel ya shaida wa wakilinmu cewa rundunar tana bakin kokarinta wajen yaki da masu satar mutane da sauran masu aikata laifuffuka. Ya ce sun kama wadansu daga cikin masu satar mutane kuma har an gurfanar da su a gaban kotu. Ya ce ba gaskiya ba ce a ce ’yan sanda suna sakin wadanda aka kama kan zargin satar mutanen domin a cewarsa ba a bayar da belin wanda aka kama da kan zargin satar mutane.
Ya ce su ma jama’a suna da nasu laifin, domin a lokuta da dama kafin ’yan sanda su kammala bincike sai ka ga ’yan uwan wadanda aka sace sun biya kudi don su karbo dan uwansu. Ya ce ’yan sanda na iyakar kokarinsu don dakile matsalar satar jama’a amma jama’a na dari-dari wajen bai wa ’yan sanda hadin kai.