Satar N660m: An tsare shugabannin ƙananan hukumomin Kano 3
Sun amsa laifin karkatar da kuɗaɗen zuwa aljihunsu
An tsare shugabannin ƙananan hukumomi uku kan badaƙalar Naira miliyan 660 na kwangilar aikin samar da ruwa a Jihar Kano.
Hukumar Yaki da Rashawa da kuma Karɓar Korafi ta Jiahr Kano (PCACC) ta tsare shugabannin ƙananan hukumomin ne bayan da suka amsa laifin karkatar da kuɗaɗen zuwa aljihunsu.
Shugabannin kananan hukumomin su ne, shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdulaziz Sulaiman, da na Bebeji, Basiru Abubakar da kuma takwaransu na Ƙaramar Hukumar Garko, Gambo Isa.
A halin yanzu dai suna can suna amsa tambayoyi a gaban jami’an binciken hukumar tare da wasu mutane 19.
- Kamfanin China ya ƙwace jirgin Najeriya na 4 a Kanada
- ’Yan bindiga na neman N50m kan mutane 10 da suka sace a Zamfara
- NAJERIYA A YAU: Gudummuwar ‘Yan Najeriya Wajen Cin Hanci Da Rashawa
Mutanen 19 sun haɗa da masu muƙamin ma’aji, manyan shugabannin sashen kula da Ruwa da Tsaftar Muhalli (WASH) da sauran manyan jami’ai a ƙananan hukumomin da badaƙalar ta shafa.
Ana zargin jami’an da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen a wani lokaci ma har da cirar su a tsabar daga bakuna.
A halin yanzu dai hukumar PCACC ta yi nasarar ƙwato Naira miliyan 10 daga cikin Naira miliyan 660 ɗin da ake bincike a kai, a cewar wasu majiyoyi.
Kazalika sun ce an ba da Berlin shugabannin ƙananan hukumomin, amma ba su kai ga cika sharuɗɗan belin ba \, a lokacin da muka samu wannan rahoto.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta saki Musa Garba Kwankwaso — ɗan uwa ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso — sa misalin ƙarfe 9nna daren ranar Alhamis, da sharaɗin zai koma ranar Litinin.
Garba Kwankwaso na fuskatar bincike a hukumar kan zargin sa da hannu a badaƙalar karkatar da Naira miliyan 440 na sayen magunguna a kananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.