Satar waya ta addabi masallatai a Ibadan
Allah Ya shiryar da su daga aikata irin wannan mummunan aiki a cikin watan Ramadan da bayansa.
A farkon makon nan ne al’ummar Musulmin suka fara yin sallolin Tahajjudi domin roƙon Allah (SWT) biyan buƙatu da neman rahama da gafara a cikin dararen goma na karshen watan Ramadan.
Sai dai kuma a irin wannan lokaci ne wasu ke yi wa masallata da sauran bayin Allah sata.
Kamar yadda hakan ya faru ga wata mata mai suna Surayyat Ahmed wadda aka sace wa wayar salularta kirar iPhone XR a lokacin da ita da sauran mata ke tsaka da sallar Tahajjud cikin dare ranar Lahadi a Babban Masallacin Unguwar Sabo mazaunin Hausawa a birnin Ibadan Hedikwatar Jihar Oyo.
Tun cikin daren ne limaman da suka jagoranci Sallar suka fara cigiyar wayar ba tare da gano ta ba, lamarin da ya sa jama’a suka fara zargin an sace ta ce.
Amma a yammacin ranar Litinin sai wata mata sanye da hijabi da ba a san ko wace ce ba ta ziyarci gidan da Surayyat take zaune ta mika wayar ga wani karamin yaro cewa ya kai cikin gidan ba tare da ambaton sunanta ba.
Binciken Aminiya ya nuna cewa a kwanan baya irin wannan lamari ya auku a wajen musabakar karatun Alkur’ani a inda aka sace wa wata yarinya mai suna Fatimat wayarta ita ma a Unguwar Sabo Ibadan.
Haka kuma an yi irin wannan satar wayar a Makabartar Akinyele a Ibadan lokacin da Musulmi suke binne gawar wani dan uwa da ya rasu.
Lamarin ya auku ne a lokacin da daya daga cikin masu haƙar kabari ya miƙa wa wani mutum wayarsa cewa ya riƙe masa.
Bayan kammala aikin haƙar kabarin ne ya nemi mutumin ya kasa gane ko wane ne.
Sake bulllar barayin waya a kwanakin karshe na Ramadan mai albarka abin takaici ne a cewar Babban Limamin Izala a Jihar Oyo, Sheikh Sani Haruna.
Kuma ya ji takaicin ganin Musulmi na aikata irin wannan mummunan aiki a wuraren ibada da makabarta.
Ya ja kunnen Musulmi masu aikata irin wannan danyen aiki da cewa: “Su ji tsoron Allah kuma su yi amfani da lokacin zumin Ramadan su tuba kafin hushin Ubangiji ya fada kansu.
“Kada su bari wannan dama ta subuce masu ba tare da sun tuba sun roki gafarar Allah ba,” in ji shi.
Shehin Malamin ya bayar da shawarar kada a yi bincike don gano matar da ake zargin ta sace wayar a cikin masallaci tunda Allah Ya sa ta dawo da ita.
“Tun da Allah Ya shiryar da ita ta gane kuskurenta kuma ta dawo da wayar da kanta, bai dace a yi wani bincike don tonon silili ba.
“Kamata ya yi a ci gaba da yi wa irinsu addu’ar Allah Ya shiryar da su daga aikata irin wannan mummunan aiki a cikin watan Ramadan da bayansa.”