Satar waya ta ja wa kafinta daurin shekara 2 a gidan yari

Barawon ya roki kotun da ta masa sassauci kan hukuncin da aka yanke masa.

Satar waya ta ja wa kafinta daurin shekara 2 a gidan yari

Kotu

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a yankin Kubwa a Abuja, ta yanke wa wani kafinta mai shekara 27 daurin shekara biyu a gidan yari saboda satar wayar hannu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Jibril ya yanke wa kafintan hukuncin bayan amsa laifin satar wayar da ya yi.

Jibril, ya yanke hukuncin ba tare da ba shi zabin tara ba, sannan ya umarci wanda aka yanke wa hukuncin da ya koyi dabi’u masu kyau a yayin zaman da zai yi a gidan yarin.

Tun da farko dai, mai gabatar da kara a gaban kotun, Babajide Olanipekun, ya bayyana wa kotun cewar, wani Ugwanyi Ugochukwu ne ya shigar da kara a ofishin ’yan sanda a ranar 16 ga watan Oktoban da muke ciki.

Olanipekun ya ce kafintan ya sace masa waya kirar Tecno lokacin da ya ke bacci, wacce darajarta ta kai kudi N65,000.

Mai gabatar da karar, ya kuma ce an cafke shi yayin da ya ke kokarin tserewa, kuma ya amsa cewar wannan ba shi ne karon farko da ya taba aikata irin wannan laifin ba.

Laifin, a cewar mai shigar da karar ya saba da sashe na 287 na kundin laifuka na ‘Penal Code’.

Sai dai barawon ya roki kotun da ta sassauta masa, inda ya yi alkawarin guje wa aikata irin wannan laifin a nan gaba.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu