Satar wayoyin iPhone 2 ta janyo wa matashi hukuncin bulala 12
Wata Kotun Majistire da ke Jihar Kaduna, ta bayar da umarnin yi wa wani matashi bulala 12 bayan samunsa da laifin satar wayoyin salula biyu samfurin iPhone. Alkalin Kotun mai suna Ibrahim Emmanuel, ya ce an yanke wa matashin wannan hukunci bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Za a dauke ruwan famfo […]
Wata Kotun Majistire da ke Jihar Kaduna, ta bayar da umarnin yi wa wani matashi bulala 12 bayan samunsa da laifin satar wayoyin salula biyu samfurin iPhone.
Alkalin Kotun mai suna Ibrahim Emmanuel, ya ce an yanke wa matashin wannan hukunci bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Mai sharia Emmanuel ya yanke wa matashin dan shekara 19 hukuncin bulala a bainar jama’a bayan ya saurari karar da aka shigar.
Matashin wanda mazauni ne a unguwar Degel da ke Jihar Kaduna, ya haura gidan wani mai suna Hassan Liman inda ya saci wayoyin biyu samfurin iPhone da darajarsu ta kai 350,000.
Bayanai sun ce matashin ya aikata wannan laifi ne a ranar 6 ga Oktoba kamar yadda dan sandan mai shigar da kara a gaban kotun ya gabatar.
A karshe dai alkalin ya ce sun yanke masa hukuncin ne bayan wanda ake tuhuma ya amsa laifin ba tare da batawa hukuma lokaci ba sannan kuma ya roki da a sassauta masa.