Satar zati a kafafen sadarwa na zamani (13)
Dokoki don yakar Satar Zati a kafafen sadarwa Daga bayanan da masu karatu suka karanta a baya tun fara wannan kasida mai tsayi, za su fahimci irin munin da wannan mummunar ta’ada take dauke da shi a fannin rayuwar daidaikun mutane da tattalin arzikin kasa a jumlace da mutunci da nagartar rayuwa da kuma fannin […]
Dokoki don yakar Satar Zati a kafafen sadarwa
Daga bayanan da masu karatu suka karanta a baya tun fara wannan kasida mai tsayi, za su fahimci irin munin da wannan mummunar ta’ada take dauke da shi a fannin rayuwar daidaikun mutane da tattalin arzikin kasa a jumlace da mutunci da nagartar rayuwa da kuma fannin tsaron lafiya da al’umma da kasa baki daya. Wannan ya ja hankalin kasashe da dama a duniya wajen samar da dokokin da za su yaki wannan nau’in ta’addanci.
Daga cikin kasashen da suka samar da dokoki akwai kasar Amurka, wacce ta fi kowace kasa yawan dokoki kan kowane irin nau’in barna da ka iya faruwa ta wannan kafa. Wannan ba abin mamaki ba ne ta la’akari da cewa ire-iren wadannan nau’ukan ta’addanci sun fi faruwa a can ne, sanadiyyar ci gaba da kuma habakar fannin a nahiyar ma baki daya. A cikin kasidarmu mai taken: “Shahararrun Samame Kan ’Yan Dandatsa,” wacce muka buga a shekarar 2010, mun kawo sunaye da bayanan ire-iren mutane da hukumomin Amurka suka kama, tare da gurfanar da su a gaban kuliya, inda a karshe aka yanke wa da yawa cikinsu hukuncin zaman gidan maza ko tara mai dimbin yawa.
Bayan dokokin da ta samar har wa yau, gwamnatin Amurka ta samar da hanyoyin wayar da kan jama’a kan matsalar Satar Zati, da irin abin da take haddasawa na tashin hankali da kuma kafofin da ’yan kasa za su je idan haka ta kasance da su. Hukumar tsaro ta Amurka ta gina shafin yanar sadarwa wanda a can take wayar da kan jama’a. A cikin wannan shafi ta tanadi abubuwa da dama da za su taimaka wa mutane idan an sace musu zatinsu, musamman wadanda aka aikata ta’addanci da bayanansu. Akwai bayanai kan hanyoyin da za su bi wajen wanke kansu da neman shawarwari da sauransu. Mai karatu na iya isa wannan shafi na kasar Amurka ta wannan adireshi: http://www.identityTheft.gob. Wannan ya kamata ya zama abin koyi ga gwamnatin Najeriya. Domin kamar yadda bayani ya gabata a makonnin baya, bayan kasar Amurka da Ingila, kididdiga ta tabbatar da cewa babu ’yan kasar da ke aikata wannan laifi irin ’yan Najeriya. Dama mun sani, tuni sunan kura ya baci tun tana karama.
Bayan kasar Amurka, akwai kasashen Ingila da Ostireliya da Kanada da Faransa da Hong Kong, da Indiya da Filifins da Suwidin da wasu kasashe ma. Daga cikin kasashen Afirka kuma akwai kasar Kenya wacce ta samar da nata dokar cikin wannan shekara (2018), sai kuma Najeriya. A namu bangaren, Najeriya ta samar da doka a shekarar 2015, wanda za ta yi yaki da nau’ukan ta’addancin da ake aikata su ta hanyar kwamfuta musamman; ya alla mai dauke da Intanet ne ko mara Intanet.
Wannan doka mai suna: “Nigeria Cyber Crime Act, 2015,” wacce tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rattaba wa hannu, tana dauke da dokoki ne masu yawa, kuma ta fi karkata ne ga irin laifuffukan da ake aikatawa wajen satar bayanai ta hanyar Dandantsa (Hacking). Kuma dokar ta yanke hukuncin dauri a gidan yari daga shekara 5 zuwa shakara 20, iya gwargwadon girman laifi. Sai kuma tara a matakin laifi daban-daban, shi ma daga abin da ya kama daga Naira miliyan daya har zuwa miliyan 20 duk na ciki.
Amma dokar ba ta yi magana a kan tsarin ayyukan laifi da suka shafi “Satar Zati” ba. Duk da cewa alkali na iya daure mutumin da ya yi hakan sanadiyyar sato bayanan jama’a ta hanyar sace kwamfuta ko barkowa cikinta ta hanyar amfani da wata manhaja, ko lalata bayanan da ke dauke cikin kwamfutar. Amma ta hanyar laifi mai sunan “Satar Zati” kam, dokar ba ta tabo bangaren ba. Har wa yau wannan doka ba ta tabo abin da ya shafi kazafi da kushiya mara dalili da kuma cin zarafi ko batanci da wani zai iya yi wa wani ta hanyar kafafen sadarwa na zamani ba. Idan mutum ya aikata wani abu mai alaka da hakan, sai dai hukuma ta yi masa hukunci da dokokin kazafi a zahirin rayuwa. Hakan kuma na bukatar bincike na musamman don tabbatar da laifin da aka yi ta hanyar kafar sadarwa – Gidan yanar sadarwa ne ko shafin sada zumunta – da shaidu da komai, wanda wannan ba karamin aiki ba ne.
Wannan ya sa daya daga cikin ’yan Majalisar Dattawa mai suna Sanata Bala Ibn Na-Allah ya yi yunkurin samar da wata doka da za ta magance hakan ta hanyar kudirin da ya samar a majalisar, amma wannan kudiri bai samu hayewa ba. A karshe ma dai kashe kudirin aka yi saboda rashin amincewar sauran mambobi da kuma korafe-korafen da ’yan kasa suka yi ta yi, musamman ’yan jarida masu zaman kansu.
Don haka, a halin yanzu dai doka daya ce muke da ita a Najeriya, wacce ke yaki da satar bayanai ko salwantar da su ta hanyar kwamfuta da Intanet. Ita kanta wannan doka a halin yanzu wadansu daga cikin masana masu sharhi kan harkokin yau da kullum suna korafin cewa dokokin da ke cikinta sun yi tsauri, sannan ba ta tattaro galibin laifuffukan da aka fi aikatawa a kafafen sadarwa na zamani ba a Najeriya. Da yawa cikinsu suna kira ga hukuma cewa a sake bitar wannan doka don fadada ta da rage kaifinta.
Sai dai ni a ra’ayina, ko an yi bitar wannan doka a rage mata kaifi, an kuma fadada laifuffukan da ke cikinta, muddin ba sake salon tsarin aiki da doka aka yi a Najeriya ba, ba abin da wannan bitar ko ma samar da dokar zai fa’idantar. Dalilina a nan shi ne, muna da dokoki da dama a Najeriya kan abubuwa daban-daban, amma babbar matsalar kasarmu ita ce, ba a sa ido wajen tabbatar da jama’a sun bi doka sau-da-kafa. Wannan abu na farko ke nan.
Dalili na biyu shi ne, wannan doka da aka samar ta yaki da tu’annati ta hanyar kwamfuta da sauran kafafen sadarwa na zamani, tana bukatar bincike mai zurfi, ta hanyar kwarewa a fannin, wadanda suke bukatar zurfin ilimi a fannin sadarwa da dokokin kasa, kafin tabbatar da mai laifi. Domin idan yanzu misali mutum ya yi amfani da kwarewarsa ta fannin sadarwa, ya kutsa cikin wata kwamfuta da ke Najeriya, ya aikata ta’addanci. Tabbatar da cewa shi ne ya aikata hakan, ba karamin aiki ba ne.
Domin dan Dandatsa na iya amfani da wata kwamfuta da ke wata kasa daban, ya umarce ta ta isar masa da sako zuwa kwamfutar da yake son kutsawa cikinta, ko ya aiwatar da sadarwa tsakaninsa da ita, ta hanyar wancan kwamfutar da ke wata kasa. Ka ga nan, idan ka duba, zahirin dubawa, ba za ka ga sawunsa ba a matsayinsa na dan Najeriya, ba kuma za ka ga adireshin kwamfutarsa ba (IP Address) wajen aikin, sai dai na wancan kwamfutar da ya mallake. Bayan haka, yana iya amfani da manhajar da ke layance adireshin kwamfuta, wato: “Connection Encryption System,” wajen ziyartar kowace irin kwamfuta ce a duniya, ba za ka taba ganin alamar shi ya yi hakan ba.
A nan ba wai cewa nake ba a iya gane wadannan nau’ukan laifuffuka ba ne har abada, a a, ana iya ganewa, amma sai an yi amfani da kwarewa na hakika a fannin sadarwa da kuma kayan aiki masu tsada da za su taimaka wajen gano “hakikanin” mai laifin, ba wai kwamfutar da ta aikata laifin ba. Samuwar hakan kuma a Najeriya a halin yanzu, ba abu ba ne da yake cikin damuwar hukuma. Wannan zai faru ne saboda nau’ukan matsalolin da kasarmu ke fuskanta a bangaren tattalin arzikin kasa da kuma tsaro.
Fina-Finai da littafai kan Satar Zati
Saboda shahara da dadewar wannan nau’i na ta’addanci a duniya, akwai wasu fina-finai da aka yi su don fadakar da jama’a kan haka. Bayan fim ma, akwai littafi na musamman wanda shi ne ya gabata kafin bayyanar tsarin fim a duniya. Wannan littafi mai suna: The Prisoner of Zender, an rubuta shi ne a 1894, shekara 124 ke nan yanzu da rubuta littafin. A cikin littafin an ba da labarin yadda wadansu abokan hamayyar wani Sarkin gargajiya da ake gab da nadawa bayan rasuwar wanda ya gada, inda masu hamayyar suka sa masa sinadarin maye a cikin abinci a jajibirin nadinsa. Kuma a al’adar wannan al’umma, duk Sarkin da ya kasa halartar ranar nadinsa, to, sarautar ta wuce shi ke nan.
’Yan uwansa da suka gan shi a buge, irin buguwar da ko gari ya waye ba zai iya wartsakewa ba, sai suka san lallai makirci ne wannan. Don haka suka je suka yi hayar wani dan kasar Ingila da ke bakunta a garin, wanda ta duk inda ka kalli Sarki bugagge, ba yadda wannan Ba’ingile ya rage shi. Kamarsu daya, kamar an tsaga kara. Shi suka dauko a boye, aka yi masa nadi a matsayin shi ne Sarkin, kuma shi aka rantsar, da haka suka sha.
Fim na farko kuma shi ne The Stolen Identity, wanda aka shirya shi a 1953. A cikin wannan fim dai wata baiwar Allah ce ta sace wa wani bawan Allah zatinsa, inda take ta amfani da suna da bayanansa a duk inda ta je. Har ta kai ga an dauka ita ce hakikanin mai sunan. Sai Fim na karshe mai suna: Idnetity Thief. An shirya wannan fim ne a kasar Ostiriya da ke Nahiyar Turai ta yanzu a shekarar 2013. Kuma shi ma, kamar sauran, maudu’insa shi ne kan satar zati da munin hakan cikin al’umma, musamman na wannan zamani.