Satar zati a kafafen sadarwa na zamani (17)

Sannan ka zama mai taka-tsantsan wajen tantance gidan yanar sadarwa sahihi daga jabunsa. Akwai gidajen yanar sadarwa da miyagu ke budewa na musamman, ta hanyar kwafar gidajen yanar sadarwa sanannu a duniya, don yaudarar masu ziyara da sace musu bayanai. Hatta galibin tallace-tallacen da kake gani a shafukan Facebook, idan ka latsa su da yawa […]

Satar zati a kafafen sadarwa na zamani (17)

Satar zati a kafafen sadarwa na zamani (17)

Sannan ka zama mai taka-tsantsan wajen tantance gidan yanar sadarwa sahihi daga jabunsa. Akwai gidajen yanar sadarwa da miyagu ke budewa na musamman, ta hanyar kwafar gidajen yanar sadarwa sanannu a duniya, don yaudarar masu ziyara da sace musu bayanai. Hatta galibin tallace-tallacen da kake gani a shafukan Facebook, idan ka latsa su da yawa daga cikinsu za su zarce da kai wani jabun gidan yanar sadarwa ne. Wannan tsari shi ake kira “Phishing.”

A dandalin Facebook akwai shafuka na bogi masu dimbin yawa, kamar yadda bayanai suka tabbatar kuma muka sha nanatawa. Daga cikin ire-iren wadannan shafuka akwai wadanda ke dauke da tayi ga jama’a, cewa duk wanda ya “So” (Like) ko ya “Yada” (Share) wani hoto ko bidiyo da aka turo, to, za a ba shi tikitin jirgin sama kyauta! Wannan ya fi shahara ne a galibin kasashen Turai. Sai dai dole mu fadaka mu ma, domin idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, sai ka nemi kogi ka yi alkafira a cikinsa don jike naka gemun.

Tsarin “Like” da “Share” a Facebook suna da amfani sosai, kamar yadda kuma suke da matukar cutarwa ga wanda bai iya mu’amala da su ba. Idan ka ga irin wadannan hotuna ko bidiyo ko bayanai masu dauke da irin wannan ta yi na cewa idan ka yi “Like” ko ka yi “Share” din shafin, za a ba ka kyautar abu kaza, kada ka latsa. Domin ire-iren wadannan shafuka da suke dauke da wannan tayi, shafukan karya ne.  Watakila ka ce mini ai shafuka ne na kamfanonin jiragen sama sanannu, irin su: “British Airways” ko “KLM” ko “Katar Airways” ko “Emirate Airways” ko kuma a daya bangaren ka ga kamfanoni irin su “Arik Air” ko “Chanchangi Airlines” ko “IRS Airlines” ko kuma “Azman Air,” a Najeriya ke nan. Eh, sunayen kamfanoni ne da ake da su amma shafukan da ke yin wannan tayin, shafukan bogi ne ba shafukan hakikanin kamfanonin ba ne. Masu wannan ta’ada mummuna suna gina shafin yanar sadarwa ne na musamman, mai dauke da bayanai iri daya sak da na kamfanin da suke son kwafowa, sannan su hankado bayanan da suke son yaudarar jama’a da su dauke da adireshin wannan shafi na bogi.

Idan ka ga haka, kada ka matsa “Like” kuma kada ka yi “Share,” in kuwa ba haka ba, za ka gwammace kidi da karatu. Ma’ana da zarar ka matsa za a zarce da kai ne shafin can na bogi da aka tsara, sannan a bukaci bayanan katin asusunka na banki (ATM Card) da lambar wayarka da sauran bayanai masu muhimmanci a rayuwarka. Kafin ka san me ke faruwa, aikin gama ya gama. Watakila bayan karanta wannan bayani ka ce, “To ai yanzu na waye, zan matsa in je can shafin in ga abin da ke faruwa.” Wannan kuskure ne mai girman gaske, domin ba ka da aminci a hakan ma, kana iya zuwa ka rudu da irin tsarin da suka yi amfani da shi na yaudara.  Ka sani, mai son kayanka ya fi ka dabara, jama’a, mu fadaka!

Taka-tsantsan wajen saukar da manhaja

Manhajojin kwamfuta ko na wayar salula da ake saukarwa kyauta, suna nan birjik, kuma bayan fa’ida ko alfanun da suke dauke da su, a daya bangaren suna tattare da matsaloli masu girman gaske. Ko kuma in ce hadari mai girman gaske. Hadarinsu kuwa shi ne, na farko dan Adam ne ya gina su kuma da manufa ta musamman.

’Yan Dandatsa masu neman bayanan mutane a sauwake sukan gina manhaja ce, wacce a zahirinta za ka ga tana dauke da fa’idoji masu girman gaske. Amma a daya bangaren kuma da zarar ka loda wa kwamfuta ko wayarka ta salula, za ta ci gaba da kwasan bayanan da suka dangance ka ne kai-tsaye, tana aika wa uban gidanta; kai ba ka sani ba. Babbar matsalar ma ita ce, idan ba kwararre ba ne kai a fagen kimiyyar sadarwa na zamani, tantance ire-iren wadannan manhajoji daga manhajoji ingantattu abu ne mai wahala kwarai da gaske.  Idan ka yi kuskure ka saukar da manhajar wayar salula ko kwamfuta mai dauke da ire-iren wadannan tsare-tsare na leken asiri, duk abin da kake rubutawa ko karba a kan wayarka ko kwamfutarka, tana nadewa ne, ba tare da saninka ba. Da zarar magininta ya gama tara bayanan da yake bukata, sai dai ka ji ana sanar da kai cewa…

 

Taka-tsantsan wajen rajistar shafi a dandalin sada zumunta

Hanya mafi sauki wajen samun jama’a a Intanet ita ce ta shafuka ko dandalin sada zumunta. Hakan ya faru ne saboda dalilai da dama. Mafi girma daga ciki shi ne irin tsarin da muhallin ke da shi. Da zarar ka mallake shi ba tare da canja komai daga cikin tsare-tsaren da maginansu suka yi ba. Wannan ya sa dole a matsayinka na mai son zaman lafiya, ka san me ya kai ka wajen, sannan mece ce manufarka? Amsar wadannan tambayoyi ne za su tabbatar da hakikanin shafinka. Don haka da zarar ka zo rajista, za a bukaci ka bayar sunan da kake son amfani da shi, wanda da shi ne manhajar dandalin za ta yi amfani wajen hada alaka tsakaninka da wadanda take ganin kuna da kamanceceniya. Za a bukaci adireshin da kake zaune da lambar wayarka da adireshinka na I-mel da shekarar haihuwa da matsayinka a rayuwa da tarihin karatunka da hotonka.

Dukan wadannan bayanai ana bukatarsu ne don gina zatinka a dandalin da kuma dauko wadanda kuke da kama na adireshi ko karatu ko zaman gari ko kasa daya, don bijiro maka da su. Wannan ita ce babbar manufar samar da dandalin Facebook; hada alaka tsakanin mutanen da ke da alaka ta zahiri.

Wadannan bayanai naka ne Dan Dandatsa ke bukata don sace maka zati. Kuma a ka’idar Dandalin Facebook misali, muddin ka bude sabon shafi, to, duk wanda ke abota da kai zai ga da yawa daga cikin wadannan bayanai naka. Amma akwai bangaren “Settings” wato inda tsare-tsaren shafinka suke. Kana iya zuwa wurin, ka boye da yawa daga cikin bayanan da ka bayar, ta yadda ko abokanka ma ba za su iya gani ba, sai wanda ya roka, in ka ga dama, ka ba shi.  In Allah Ya so, nan da wasu lokuta zan yi darasi na musamman kan yadda ake boye bayanai a Facebook.

 

Taka-tsantsan wajen yada bayanai a dandalin sada zumunta

Duk wanda ya bude shafi a dandalin sada zumunta, to, da wahala ka ga bai rubuta wani abu ba, ko da kuwa daga wajen wani ya kwafo. Wannan ita ce al’adar muhallin kuma ba hakan ba ne laifi.  Inda lamarin yake shi ne, me ka rubuta ko ka zuba a shafinka? Da yawa cikin mutane kan tona wa kansu asiri a shafukansu na dandalin sada zumunta. Su suke aibanta kansu a cikin hotuna a cikin zance. Su suke janyo wa kansu hassada, wanda a karshe zai kai ga saryar da mutuncinsu da kuma dukiyarsu. Amma ba kowa ya fahimci haka ba.

Su ’yan Dandatsa masu shawagi don kalato bayanan mutane, a ire-iren wadannan wurare, sun fi saurin sace mutum mai yawan surutu da alfahari da fadin abin da ba a tambaye shi ba kuma mara alfanu ga rayuwa ko addininsa.  Nan take sai su sa masa ido. Misali, akwai wadansu mutane, kowane irin yanayi suke ciki, sai sun rubuta a shafukansu. Idan cin tuwo suke, sai sun fada, tare da dora hoton towan ma. Idan rashin lafiya suke, sai sun fada, ba ma fada kadai ba, sai sun dauki hotonsu a kan gadon asibiti sun dora.  Idan mutuwa aka yi musu sai sun fada, ba ma fada kadai ba, hatta hoton gawar ma sai sun dora a shafinsu. Idan mota suka saya sai sun fada, sannan su dora hoton motar a shafinsu. Idan aiki suka samu, sai sun fada, sannan su dora hoton wasikar tayin aikin da aka ba su. Idan makaranta suka gama, sai sun fada, sannan su dora hoton shaidar gama karatun a shafinsu. Idan tafiya za su yi, sai sun fada, sannan su dauki hotonsu suna tukin mota, ko suna cikin jirgin sama ko na kasa, ko babur ko keke, duk su dora a shafinsu. Idan kwalliya suka yi, duk sai sun fada, sannan su dora hoton kwalliyar ko “wankan” kamar yadda Kanawa ke fadi, a yanzu, a kan shafinsu. Kuma galibinsu, kana hawa “Profile” dinsu sai ka gan su tsirara. Ma’ana ga bayanansu nan a bude, ko sutura babu. Alamar cewa ba su san manufar kasancewarsu a wannan muhallin ba ke nan. Mai karatu, idan kana cikin ire-iren wadannan mutane, ka yi hakuri. Ba manufata ba ce in aibanta ka. Shi ya sa ma ban ambaci sunan kowa ba.  Manufar ita ce fadakarwa.

 

Za mu ci gaba