Satar zati a kafafen sadarwa na zamani (18)
Dabi’a irin wannan ba ta kamaci mai hankali, mai manufa a rayuwa da al’ada ba, wanda ya san ciwon kansa. Don haka mu kiyaye. Ka sani, irin bayanan da kake rubutawa ko yadawa a shafinka, duk abokanka suna gani. Idan ba yanzu hukumar Facebook ta canja tsarin ba, hatta abokan abokanka (Friends of Friends), su […]
Dabi’a irin wannan ba ta kamaci mai hankali, mai manufa a rayuwa da al’ada ba, wanda ya san ciwon kansa. Don haka mu kiyaye. Ka sani, irin bayanan da kake rubutawa ko yadawa a shafinka, duk abokanka suna gani. Idan ba yanzu hukumar Facebook ta canja tsarin ba, hatta abokan abokanka (Friends of Friends), su ma suna gani.
Idan ka yi rubutu a shafinka na Facebook misali, jama’a na iya ganin rubutun ta dayan dalilai hudu ne. Abokanka (Friends) na iya gani, saboda a hankalce su ne amintattun mutane a gare ka. Na biyu, abokan abokanka (Friends of Friends) na iya gani, saboda amintuwar da ke tsakanin abokanka da su. Na uku, duk wanda ya ci karo da shafinka a Facebook yana iya ganin abin da ka rubuta a farfajiyar shafinka (Timeline), idan ka bar tsarin a “Public” ke nan. Sannan a karo na karshe, kana iya rubuta bayanai ka boye shi a shafinka, ba tare da kowa ya iya gani ba, sai kai kadai (Only Me). Wadannan su ne tsare-tsare da suka shafi sirrin bayanai a Facebook, wadanda mai shafi ke rubutawa. A ka’ida, idan ka bude sabon shafi a Facebook, babu wanda zai iya ganin bayanan da kake rubutawa a shafinka sai kai da abokanka kadai, sai idan ka canja wannan tsari.
Duk wannan dogon bayani dai ina so in jawo hankulanmu ne kan hadarin da ke tattare da abin da muke yi a Facebook, musamman ko Twitter ko LinkedIn ta bangaren yada bayanai da wadanda ke iya isa ga bayananmu. Duk abin da ka san zai zama aibi a gare ka nan gaba, kada ma ka taba dorawa ko rubuta shi a shafinka na Facebook ko Intanet.
Taka-tsan-tsan wajen yin abota a Dandalin Sada Zumunta
Dandalin abota irin na zamani kamar kasuwa ce, wadda a cikinta jama’a kan hadu daga ko’ina a duniya. Wannan kasuwa dai tana da hanyar shiga da ta fita, sannan akwai ka’idojin mu’amala da hukumar kasuwar ta gindaya. Amma me jama’a ke sayarwa, ko me suke tallatawa, ko me suke aiwatarwa a ciki, ko kuma mutanen kirki ne ko na banza a kasuwar? Wannan duk ba damuwar hukumar kasuwar ba ce, har sai an kai mata kara. Wannan ya sa jabun mutane da jabun shafuka suka fi yawaita a gidajen yanar sadarwar sada zumunta na Intanet. In kuwa haka ne, shin mai karatu, ko ka taba zama ka lura da su wane ne kake mu’amala da su a shafukanka na sada zumunta?
Babbar manufar bude shafukan sada zumunta musamman na Facebook, zan kara nanatawa, ita ce don mutane da suka san junansu a gari guda, ko wata makaranta da suka taba yi, ko wani taro da suka taba haduwa na addini ko kasuwanci, su samu damar sake haduwa da juna don sadarwa kuma alakarsu ta ci gaba. Amma ba a bude wadannan shafuka don yin mu’amala ko abota da mutumin da ba ka taba saninsa ba. Amma haka lamarin yake a aikace? Amsar ita ce a’a.
Daga cikin manyan matsalolin da ke jawo hasarar dukiya da mutunci a dandalin abota akwai yawan karbar abokai barkatai ba tare da tantancewa ba. Tabbas ba abu ba ne mai yiwuwa a ce dole sai wanda ka sani a zahirin rayuwa kadai za ka yi abota da shi amma kuma wannan ba lasisi ba ne wajen karbar kowane irin kwamacala da sunan aboki. Masu neman abota da mutum a dandalin sada zumunci sun kasu kashi-kashi. Akwai masu neman abota don karuwa da kai, musamman idan ka shahara wajen rubuce-rubuce masu fa’ida a addini da rayuwa ko siyasa da al’adu. Wannan daidai ne kuma yana da kyau.
Wannan ya fi shahara a bangaren malaman addini da siyasa da sauran fannonin ilimi. Akwai masu nemanka da abota saboda sun sanka ne a zahirin rayuwa. Wannan ya yi daidai da manufa da kuma al’adar Facebook. Misali, akwai masu nemanka da abota kawai don sun sanka a suna sanadiyyar shahara ko sun taba jin sunanka a wajen wadansu amma ba su taba ganinka ba. Wannan, ta wata fuskar kuskure ne, musamman idan ba mutanen kwarai ba ne su, ko kai da ake nemanka da abotar ba mutumin kirki ba ne. Wannan ya fi shahara a bangaren ’yan fim da marubuta littafan soyayya da shahararrun ’yan siyasa da ’yan jarida.
Har wa yau, akwai masu nemanka da abota saboda su samu damar kusantarka don wata manufa mummuna. Wannan ya fi shahara a bangaren ’yan dagaji, masu mugun nufi ke nan. Suna kusantar ’yan siyasa kamar yadda suke kusantar shahararrun mata da maza da ke wadannan wurare. Akwai kuma masu nemanka da abota kawai don sun ga garinku daya ko jiharku daya ko kun yi makaranta daya – koda ba tsararka ba ne ko kuma kuna da ra’ayin siyasa ko addini iri daya. Akwai kuma masu nemanka da abota ba don komai ba, sai don kyan hoton da ka sa a shafinka, ko hotunanka da suka gani, ko irin nau’in sunanka.
Wannan ya fi shahara a bangaren mata, inda maza musamman samari ke nemansu da abota saboda kyan hoton da ke shafukansu ko sunayensu kawai, ba don wata karuwa mai fa’ida ba. A karo na karshe kuma, akwai masu nemanka da abota don manufar kasuwanci. Da zarar ka karbe su kawai za su ta jefo maka tallace-tallace a shafinka da sunan “Tagging.”
Duk wanda za ka karbe shi a matsayin aboki, dole ne ka san daga ina yake? Idan ka taba saninsa, shin mutumin kirki ne? Idan ba ka taba saninsa ba, akwai alamar gyaruwa tare da shi? Ta dalilin wa ya sanka? Mutum nawa ne kuka hada a matsayin abokai tsakaninka da shi (Mutual Friends)? In kun hada abokai, wadanne iri ne? Masu mutunci ne? Wadanne irin hotuna ne a shafinsa? Shin, hakikanin hotonsa ya sa? In eh, a wace siffa yake? In a’a, hoton mene ne a profile dinsa? Akwai nau’ukan hotuna kusan 100 a Facebook wadanda duk inda na gan su, na san jabun hotuna ne, kuma masu shafukan ba hakikaninsu ba ne. Sannan kuma dole dayan biyu; ko dai ya zama ’yan madigo ne ko wani kato ne ya bude shafin da sunan mata. Ka sani, irin yanayin abokanka irin yanayinka. Masu iya magana na cewa, sai hali ya yi daidai ake abota. Ana iya gane nagartarka ce da zamaninka da kuma irin mutanen da ka zauna da su. Shi ya sa, a tunani mai saiti na addini, babu wadanda suka kai sahabban Annabawa nagarta bayan gushewar Annabawan.
Rashin tantance mutanen da za ka karba a matsayin abokai ko nemi abotarsu, na taimakawa wajen jajibo miyagu kusa da kai. Kuma wannan zai ba su damar ribatarka ta hanyar abin da kake zubawa a shafinka.
Haka idan da kowa kana iya hira a shafinka, tare da fayyace musu rayuwarka gaba daya, babu sirri. Da yawa cikin miyagu kan bukaci hira da mutanen da suke son zambata, don kara fahimtarsu da kuma rarakar bayanan da suke nema kai-tsaye daga gare su. Wannan tsari shi ake kira: “Social Engineering” a ilimin kimiyyar sadarwa na zamani. Idan ya zama kowa ka tashi hira da shi sai ka fayyace masa rayuwarka da inda aka haife ka da garinku da sana’arka da watakila ma har da ba shi lambar waya ba tare da sanin hakikaninsa ba, wannan kana haka wa kanka ne rami mai zurfi.
Yadda ka zama mai kaffa-kaffa wajen yada bayanai, ka zama mai taka-tsan-tsan wajen yin abota ta mutane. A duniyar Intanet babu muhalli mafi hadari irin dandalin sada zumunta.