Sau 8 aka aura min ’yan Boko Haram —Ɗalibar Chibok Mai Juna-biyu
Ta bayyana yadda ake tsare ‘yan mata a sansanin Boko Haram da ke dajin Sambisa.
Ɗaya daga cikin ’yan matan Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014, mai suna Ihyi Abdul, a Jihar Borno, ta ce an tilasta mata auren maza takwas yayin da ta ke hannun Boko Haram.
Aminiya ta ruwaito yadda Rundunar Operation Haɗin Kai ta miƙa yarinyar Chibok da aka ceto tare da wasu mutum 332 ga gwamnatin Jihar Borno.
- Zanga-zanga: Majalisar Koli Ta Shari’ar Musulunci Ta Gargadi Matasa
- DAGA LARABA: Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama
Mutum 332, ciki har da mata 110 da yara 220, an ceto su ne a yankin Bama-Pulka yayin wani samame da dakarun soji suka kai dajin Sambisa.
A yayin wani taron a sansanin Maimalari da ke Maiduguri, Manjo Janar Waheed Shuaibu, Kwamandan Operation Haɗin Kai, ya ce an ceto Ehi Abdul mai shekara 27, wacce ke ɗauke da juna biyu na wata uku, a ranar Talata tare da ’ya’yanta biyu a dajin Sambisa.
Da ta ke jawabi ga manema labarai a hedikwatar Operation Haɗin Kai a Maiduguri, ta ce, “Na yi tafiyar tsawon kwanaki kafin na isa wani wajen da sojojin Najeriya suke, inda suka karɓe ni da ’ya’yana.
“Na auri maza takwas kuma na haifi yara uku. Ban yi ƙoƙarin tserewa ba a baya saboda ban shirya tserewa ba sai a yanzu.
“Ba a ajiye ‘yan matan Chibok a sansani ɗaya, kuma ban san dalilin da ya sa ake tsare wasu tsare ba. Wasu daga cikinmu sun zaɓi zama a Sambisa, yayin da wasu ba su samu damar tserewa ba.
“Game da ilimi, ba zan iya cewa komai ba a yanzu, amma ba ni da tabbacin cewar zan iya ci gaba da karatu ba.”