Sau takwas ana korarmu daga gidan haya saboda fitinar matata – Magidanci

Wani magidanci mai suna Nurudeen Adeoye da ke sana’ar acaba ya roki wata kotu a Ibadan ta raba aurensa da matarsa mai suna Iyabo saboda yawan fitinarta. dan acabar ya  ce ,atar tasa ta yi sanadiyyar korarsu daga gidajen haya daban-daban har 8 a zaman aurensu na tsawon shekara 17. Ya ce, yawan fada da […]

Sau takwas ana korarmu daga gidan haya saboda fitinar matata – Magidanci
Sau takwas ana korarmu daga gidan haya saboda fitinar matata – Magidanci

Wani magidanci mai suna Nurudeen Adeoye da ke sana’ar acaba ya roki wata kotu a Ibadan ta raba aurensa da matarsa mai suna Iyabo saboda yawan fitinarta. dan acabar ya  ce ,atar tasa ta yi sanadiyyar korarsu daga gidajen haya daban-daban har 8 a zaman aurensu na tsawon shekara 17.

Ya ce, yawan fada da take yi da masu gidajen da makwabta da ’ya’yansu ne ya haifar da korar da masu gidajen suka rika yi musu a lokuta daban-daban a tsawon wannan lokaci.

Cikin karar da ya shigar a gaban Kotun Gargajiya ta Oja Oba/Mapo da ke Ibadan, Nurudeen wanda ya isa kotun rike da takardun sanarwar sallama daga gidajen haya a matsayin shaida, ya ce matar tasa ta jefa shi cikin mawuyacin hali a tsawon lokacin da suke tare. Ya kawo misali da rabuwa da mutanen kirki da ya saba huldar arziki da su. Ya ce ita ce ta haddasa mummunar gaba a tsakanin ’ya’yansu da na makwabta.

“Na taba daukar wasu kudi daga cikin jakarta ba tare da saninta ba, wanda na yi amfani da su wajen biyan kudin hayar gidan da muke zaune, tare da yi mata alkawarin biyanta idan na kwashi albashina amma ta tsaya kai-da-fata ba ta yarda ba, sai dai in biya ta a wannan rana. Hakan ne ya sa ta rufe kofar gidan da muke zaune ta hana ni shiga ciki, inda na kwana a waje,” inji shi.

Magidancin ya ci gaba da cewa, “Wani abin mamaki shi ne, a wani lokaci da na yi kokarin dawo da uwargidata da muka rabu, sai Iyabo ta kekasa kasa ta ki amincewa tare da kulla mini sharri, cewa na sace mata rigar nono da zan yi tsafi don hallaka ta. Ta kai karata ga iyayenta inda suka amince da bayanan karya da ta shirga musu. A wannan lokaci ne ta fice daga gidan da muke zaune ta je ta auri wani mutum, ba tare da na sake ta ba.”

Ya ce, “Har ila yau, a kwanakin baya ta ziyarci gidana, wai ta zo ne domin taya ’ya’yanta da ke tare da ni bikin Sallar Layya, inda na ki amincewa. Hakan ne ya sa ta tayar da rikici a bainar jama’a, inda nan take makwabta suka shiga tsakani, suka kore ta.”

Ganin cewa Iyabo ta ki amsa sammacin gayyata da kotun ta aike mata sau biyu, domin ta zo ta kare kanta, Alkalin Kotun Cif Ademola Odunade ya yanke hukuncin raba auren nan take tare da gargadin matar kada ta sake waiwayar gidan tsohon mijin nata.