‘Sau uku ina tsallake binne ni a kabari’
Malam Haruna Ibrahim wani magidanci ne da ya hadu da larurar gurguntaka bayan ya girma, kafin kafar ta dawo tana yin aiki bayan ya shekara 12 da zama gurgu. Ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faro da yadda kuma aka rika shirya yi masa jana’iza bisa tunanin ya mutu har sau uku kafin […]

Malam Haruna Ibrahim wani magidanci ne da ya hadu da larurar gurguntaka bayan ya girma, kafin kafar ta dawo tana yin aiki bayan ya shekara 12 da zama gurgu. Ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faro da yadda kuma aka rika shirya yi masa jana’iza bisa tunanin ya mutu har sau uku kafin ya farfado:
Ka fara da gabatar da kanka.
Sunana Haruna Ibrahim, ni dan kauyen Maiwa ne da ke karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, ina da mata da kuma ’ya’ya 8, yanzu ina da kimanin shekara 48.
Mene ne musabbabin matsalarka ta rasa kafa?
An haife ni da kafafuna lafiya lau har na girma na kai kimanin shekara 36. Wata rana na je gonata na yi sharar gona a lokacin bazara da yamma ta yi na dawo gida lafiya lau. To washegari ne sai na ji kamar wani abu ya shige ni ina an soke ni a kafata ta hagu. Mutane sun danganta lamarin da sassabe wata itaciya da na yi a cikin gonata wanda na yi ne don neman itace da kuma karin filin noma. Sai dai ni na maida komai ga Allah a matsayin wani hukunci da Ya kaddara sai ya faru da ni. Da farko na dauki lamarin a matsayin amosanin kashi, na nemi magani amma abin bai yi sauki ba, sai kara muni yake yi, cikin mako guda sai ya kasance ba na iya tashi, idan ko na iya tashin ma sai in fadi a kasa. An kai ni asibitoci daban-daban kamar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato da na (Jami’ar Ahamdu Bello da ke) Zariya da na kashi da ke Kano, sai kuma wani mashahurin asibiti da ke Galmi a Jihar Tawa ta Jamhuriyar Nijar.
A duk wuraren nan an yi min gwaje-gwaje iri-iri amma ba a ga komai ba. Har ya kai ga hannuna ba ya iya yi mini komai koda daga hannun ba na iya yi sai an ba ni ruwa. Hanuna sai ya koma sai bari kawai yake yi, iyalina ne ke kai ni bayan daki ta cire min wando sannan ta min dahara idan larura ta kama ni.
Yaya batun ’ya’ya da sauran al’amuran rayuwa?
Dama da farko Allah Ya ba mu ’ya’ya hudu tun kafin larurar da kuma wadanda aka samu a cikin lalurar. Amma bayan nan sai haihuwa ta tsaya kuma batun mu’amala irin na tsakanin miji da mata ba ma ko tunanin wannan. Daga baya ne haihuwarmu ta dawo kasancewar ina samun kuzari a duk lokacin da Allah Ya nufe ni, sannan bayan shigar ciki kuma sai yanayin lalurar jiki ya sake ta’azzara ya zamanto ba na iya yi wa kaina komai. Kuma a wannan tsakani ne muka samu karin wadansu ’ya’ya hudu, yanzu muna da ’ya’ya 8 ke nan.
A farkon matsalar na shekara kamar uku ba na fita koda daga daki, a daki nake tare da iyali a koyaushe, a wajen nake ba-haya ta wanke mini a nan take yi mini wanka ba na ganin ko sararin samaniya bare na ga rana. Bayan na shekara kamar uku a cikin wannan hali sai na bukaci a saya mini keke wanda zan iya kwanciya a ciki ana fita da ni. A nan na ga gari ya sauya mini hatta kofar gidana sai da na ga kamar an sauya masa fasali.
A cikin hakan sau uku ana sanar da mutuwata, a na biyun da kuma na ukun sakamakon doguwar suma da nake yi za a taba ni a yi magana amma a ga shiru. A na biyun da kuma na ukun har an kai ga yi min wanka, amma bayan wanka idan aka dan saurara da kamar miniti talatin ko awa daya sai a lura na fara motsawa kafin a kai ga saka mini likkafani.
Yaya batun sana’a, ko bara ka koma?
Ban yi bara ba. Dama baya ga sana’ar noma ina sayar da magunguna irin na Musulunci wato su Habbatus Sauda’a da makamantansu. To bayan shekara hudu da wannan larura sai na shiga yawatawa da shi a kan kekena na guragu. Haka na yi ta fadi-tashi har Allah Ya sauwake mini wannan larura kamar wata uku ke nan yanzu, ana azumin Ramadan saura kamar kwana 18.
Yaya aka yi ka samu kafafunka suka dawo da aiki bayan wadannan shekaru?
Bayan na samu hanzari a wani lokaci sai na yanke shawarar ziyartar wadansu ’yan uwana a wani kauye da ake kira Garin Malamai, yana nan yamma da garin Sabon-Birni a jiharmu ta Sakkwato. To da zan kai ziyarar ban je da keken da nake hawa ba kasancewar sai na shiga mota, haka nan wani dana ya goya ni muka hau babur sannan muka shiga mota muka je. ’Yan uwan nawa sun cika da mamakin ganina ba tare da keke ba. To daga ranar ziyarar da na yi ne na fara jin hanzari kuma su kansu sun kula da hakan ganin har hannuna yana motsawa, a nan ne suka yin min tambaya ko dai akwai wani magani ne da na samu. Na ce masu a’a, ni yau shekara 8 ke nan da na rabu da shan magani a kan wannan larura na bar komai ga Allah sai abin da hali ya yi. Bayan dawowa ta gida da ranar Juma’a ta zo sai na ji jikina ya yi tsanani amma da lokacin Sallar Juma’a ya yi sai na kukuta na shafa jikina na yi alwala, aka dora ni a kan keke na je masallaci na yi Sallar Juma’a a kan keken. Bayan na dawo sai na bukaci a kai ni karkashin wata bishiya da ke cikin gidan na mike a kan tabarma ina jin jikin nan sosai, a ranar a nan na rika mirginawa a kan tabarma ana cikin haka sai Allah Ya kawo mini wani barci mai nauyi da na jima ban yi irinsa ba, har sai da aka tayar da ni aka ce an yi Sallar La’asar. Kafin nan barcina bai wuce awa daya a dare ne ko a rana tun bayan aukuwar matsalar. To bayan farkawata sai na ji yanayin jikina ya sauya, na daga hannu na ga ya mike gaba daya, har na iya jawo ruwan da ke kusa da ni sannan na yi alwala. A wajen wanke kafa sai na kula jikina ya kara sakewa domin da na jan kafra sai na ji ta taho. Na yi ta jin karin hanzari (sauki) a ranar har zuwa lokacin Sallar Magariba, sai na yi alwala na sanar da iyalina cewa zan je masallaci, sai ta ce to bari a kawo maka keke, amma sai na ce ta bar keken, na ce ki dai dauko mini wata sandata da na ke amfani da ita a farkon wannan larurar. Ta shiga daki ta duba amma ba ta gani ba, bayan na kara yi mata kwatance ne ta koma amma kafin ta fito sai na yi tsugunne na ji na tsaya a kan kafafuwana har na ji yatsun kafar sun yi karar mikewa kamar an ja su sun yi kat din nan. Daga nan sai na yunkura zan tashi na yi Bisimillah sai ga ni na kai ga yin ruku’u, na kasance a hakan na dan wani lokaci sai na dangana da tsayawa, sai na ji na mike tsaf. Ko da ta fito ta gan ni a tsaye ba ta ma iya karasowa inda nake ba saboda mamaki kafin ta taho sai na matso na karbi sanda na ce da ita zan je masallaci, abin ya ba ta mamaki sosai.
Haka nan jama’a da na fito waje, shi kansa limaminmu ya jima yana kallon ikon Allah a yayin juyowa a gyara sahu. Bayan sallama ne na je gabansa na ce da shi ina barar addu’a daga wajen jama’a a kan wannar larura da na ga alamun karshenta, Allah Ya tabbatar min, suka yi min addu’a na kama hanyar dawowa gida amma ba wanda ya yi kusa da ni saboda al’ajabi. Na dawo gida na samu waje ya cika. Ranar an yi kamar ana biki a gidana jama’a kowa murna yake yi ana ta sayan abubuwa ana sadaka, waya kuma tun daga lokacin aka fara bugo mini ana ta barka daga garuruwa daban-daban har sai da dare ya raba tukuna aka tsagaita.
Wane darasi za ka ce ka koya a tsawon wannan lokaci?
A gaskiya na koyi darussa da dama, na farko dai ya kara kusanta ni ga Allah kuma na kara gaskata cewa duk abin da mutum zai yi ya riki Allah, Shi kadai ne Mai iya sanya masa larura, Shi ne kuma zai cire maka idan lokacin cirewar ya yi. Na kuma gode wa matata da irin kulawar da ta ba ni tare da kasancewa da ni a tsawon wannan lokaci ba tare da nuna kosawa ba, Allah Ya saka mata da mafi kyan sakayya. Yanzu haka na dawo bakin sana’ata kuma na kara da koyar da matasa addini a wannan waje da ka same ni, inda wani bawan Allah ya ba ni matsuguni a nan Kubwa inda muke yin karatun.