Saudiya ta hana katar jigilar alhazai da jiragenta

katar ta yi Allah wadai da tsarin kasar Saudiya na hana jiragenta sauka da tashi a filin  saukar alhazai, inda ta ce sai dai mahajjatan kasar su yi amfani da jiragen Saudiya domin zuwa hajjin na bana. Idan ba a manta ba, tun a watan Yulin bana ne wasu kasashen Larabawa ciki har da Saudiya […]

Saudiya ta hana katar jigilar alhazai da jiragenta

katar ta yi Allah wadai da tsarin kasar Saudiya na hana jiragenta sauka da tashi a filin  saukar alhazai, inda ta ce sai dai mahajjatan kasar su yi amfani da jiragen Saudiya domin zuwa hajjin na bana.

Idan ba a manta ba, tun a watan Yulin bana ne wasu kasashen Larabawa ciki har da Saudiya suka yanke alaka da kasar katar, saboda suna zargin ta da taimakawa ta’addanci, zargin da kasar ta karyata.

kasar Saudiya ta sanar a kwanakin baya cewa za ta taimakawa kasar katar wajen dauko mahajjata kasar zuwa hajji, wanda da farko kasar katar ta yi maraba sanarwar. Amma kuma daga baya kasar ta ce bai kamata a mata haka ba.

“Sanannen abu ne cewa duk maniyyata suna zuwa hajji ne ta jiragen kasarsu, inji Ahmed al-Rumaihi wanda shi ne Daraktan yada labarai a ofishin ministan harkokin kasashen wajen katar kamar yadda kafar dillancin labarai na Reuters ta ruwaito. 

Ya kara da cewa “Ya kamata kasar Saudiya ta dage takunkumin da ta daura wa kasar katar domin mu samu damar kai mahajjata su yi hajjin bana ta hanyar da suka zaba kuma suke so wanda shi ne jiragen katar,” inji shi.

kasashen da suka yanke alaka da kasar katar sun hana jiragen kasar sauka a kasashen su, yayin da ita kuma kasar Misra ta kori ‘yan katar daga Misra.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista