Saudiyya: An haramta wa limamai karbar taimako a Ramadan
A farkon makon nan ne Hukumar Harkokin Addinin Islama ta kasar Saudiyya ta fitar da wata sanarwa, inda a cikinta ake jan kunnen limaman masallatai da kada su kabi taimako daga jama’a lokacin watan azumin Ramadan.Sanarwar ta kara da cewa duk wanda yake son ba da taimako ga masallata, to ya mika shi ga kungiyoyin […]
A farkon makon nan ne Hukumar Harkokin Addinin Islama ta kasar Saudiyya ta fitar da wata sanarwa, inda a cikinta ake jan kunnen limaman masallatai da kada su kabi taimako daga jama’a lokacin watan azumin Ramadan.
Sanarwar ta kara da cewa duk wanda yake son ba da taimako ga masallata, to ya mika shi ga kungiyoyin agaji da gwamnati ta bai wa lasisi.
Wannan yana nufin ke nan ba a yarda limamai su karbi kudin ciyarwar abincin buda baki da ake bayarwa lokacin azumi ga masallatai ba, kamar yadda kafar yada labarai ta Arab News ta ruwaito.
Har ila yau, kamar yadda sanarwar ta ce, duk wadanda suke son raba abinci lokacin azumi su nemi izini daga hukumomin lardinsu kuma wajibi ne abincin ya fito daga gidan cin abincin da yake da lasisi.
Sai dai kafar yada labaran ba ta yi karin haske ba game da dalilin da ya sa mahukuntar kasar suka dauki wadannan matakan ba.