Saudiyya: An kwantar da Sarki Salman a asibiti

Rahotanni na bayyana cewa an kwantar da sarki Salman Bn Abdul’aziz na Saudiyya saboda lalurar da ya samu a mafitsararsa. Sarki Salman ‘Dan Abdul’aziz na kasar Saudiyya ya na kwance a asibiti da ke birnin Riyadh ana yi masa gwaje-gwaje, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka sanar. Jaridun kasar Saudiyya a ranar Litinin, sun […]

Saudiyya: An kwantar da Sarki Salman a asibiti

Sarki Salman Bn Abdul’aziz na Saudiyya

Rahotanni na bayyana cewa an kwantar da sarki Salman Bn Abdul’aziz na Saudiyya saboda lalurar da ya samu a mafitsararsa.

Sarki Salman ‘Dan Abdul’aziz na kasar Saudiyya ya na kwance a asibiti da ke birnin Riyadh ana yi masa gwaje-gwaje, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka sanar.

Jaridun kasar Saudiyya a ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an kwantar da sarkin mai shekara 84 a asibiti.

Sarki Salman ya fara mulki a Saudiyya tun a shekarar 2015 kafin zamansa Sarki. Kuma ana ci gaba da yi masa gwaje-gwaje

Kamfanin dillacin labaran kasar Saudiya SPA ya bayyana cewa an kwantar da Sarki Salman asibitin birnin Riyadh, ba tare da wani cikakken bayani ba.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram