Saudiyya na azabtar da mata masu fafutuka – Amnesty
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi zargin cewa Saudiyya tana azabtar da masu fafutuka da suka hada da mata da dama. Fursunoni a Gidan Yarin Dhahban sun yi zargin cewa ana azabtar da su da lantarki da kuma zane su da bulala. Saudiyya ta kama mata da dama masu fafutuka a farkon wannan shekarar […]
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi zargin cewa Saudiyya tana azabtar da masu fafutuka da suka hada da mata da dama.
Fursunoni a Gidan Yarin Dhahban sun yi zargin cewa ana azabtar da su da lantarki da kuma zane su da bulala.
Saudiyya ta kama mata da dama masu fafutuka a farkon wannan shekarar da kuma wasu fitattun malamai.
Da BBC ta tuntubi hukumomin Saudiyya don jin ta bakinta a kan wannan zargi abin ya ci tura, sai ta ruwaito wani jami’in Saudiyya yana shaida wa Mujallar Wall Street Journal cewa “masarautar ba ta goyon bayan azabtarwa kwata-kwata.”
Kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch sun fitar da sanarwa a ranar Talatar da gabata, inda suka yi bayanin yadda ake azabtar da fursunonin.
Sanarwar Amnesty ta ce wasu masu fafutukar ba sa iya tsayawa da kafafunsu wasu kuma ba sa iya tafiya bayan da aka azabtar da su da lantarki da kuma yi musu bulala.
Ta kuma ce wata mata ta bayar da rahoton yadda wasu masu kula da wajen da ke rufe fuskokinsu suka rika cin zarafinta da neman yin lalata da ita.
Ita ma sanarwar Human Rights Watch ta fitar da sanarwar yadda ake azabtar da mutane da lantarki da zane su da kuma tilasta musu wajen runguma da sumbatarsu, kamar yadda aka yi wa akalla wasu mata uku da ake tsare da su.
An yi ta yabon Sarki Salman bn Abdulaziz Al Saud da dansa Yarima mai jiran gado Muhammad bn Salman a bara sakamakon kawo sauye-sauyen ci gaban zamani da suka hada da dage dokar haramtawa mata tukin mota.
Amma masu suka suka ce a bangare guda kuma ana murkushe masu sukar masarautar.