Saudiyya na sha’awar karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta Mata a 2035

A 2022 ne aka kafa tawagar mata ta Saudiyya, kuma ya zuwa yanzu ba ta kai ga buga gasa ko ɗaya ba.

Saudiyya na sha’awar karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta Mata a 2035

Saudiyya na sha’awar miƙa tayin karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta Mata da za a yi a 2035, kamar yadda daraktan wasannin bangaren mata ta ƙasar ta bayyana.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makonnin bayan nan ne Masarautar Saudiyya ta shigar da buƙatarta ta ɗaukar nauyin Gasar Kofin Duniya na maza da za a yi a 2034.

“Ina da yaƙinin wasannin mata da ’yan mata na da goben da za ta haskaka a Saudiyya,” in ji Monika Staab.

Tun kafin yanzu dai kungiyoyi masu da’awar kare ’yan bil’Adam ke zargin Saudiyya da take hakkin dan Adam yayin da ake ganin cewa mata ba su da cikakken ’yanci a ƙasar.

’Yan wasan kwallon kafa mata sun nuna damuwa kan jinsin da suke nema, yayin da aka riƙa suka kan shirin hukumar yawon buɗe ido ta Saudiyya da ta nemi ɗaukar nauyin Kofin Duniya na 2023 da ya gudana a Australia da New Zealand.

Daga baya Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya Fifa ta yi watsi da wannan shiri, bayan ƙasashen da suka ɗauki nauyi sun nuna rashin amincewa kan wannan tayi.

A 2022 ne aka kafa tawagar mata ta Saudiyya, kuma ya zuwa yanzu ba ta kai ga buga gasa ko ɗaya ba.

“Na shaida wa shugabannin wasanninmu cewa zai ɗauki tawagarmu ta je Gasar Kofin Duniya.

“Kuma na san suna shirin ɗaukar nauyin Gasar Kofin Duniya na maza — me ya sa ba za a ɗauki nauyin ta mata ba ta 2035?” in ji Staab.

“Yanzu muna da tawagar kamata ya yi mu fara tunkarar gasa muga ni.”

A bisa wannan batu, muddin Saudiyya ta daura harama, za ta yi takara ne da Ingila wadda ita ma take da sha’awar miƙa tayin karɓar baƙuncin gasar.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna