Saudiyya na son Amurka ta cire Sudan daga jerin ‘yan ta’adda

Kasar Saudiyya ta ce tana kokarin ganin kasar Amurka ta cire sunan Sudan daga jerin sunayen kasashen da take zargi da tallafa wa ta’addanci a duniya, domin kasar ta ci moriyar da sauran kasashen duniya ke ci. Saudiyya ta sanar da haka ne a wata ganawa da aka yi tsakanin Sarki Salman na Saudiyya da […]

Saudiyya na son Amurka ta cire Sudan daga jerin ‘yan ta’adda

Kasar Saudiyya ta ce tana kokarin ganin kasar Amurka ta cire sunan Sudan daga jerin sunayen kasashen da take zargi da tallafa wa ta’addanci a duniya, domin kasar ta ci moriyar da sauran kasashen duniya ke ci.

Saudiyya ta sanar da haka ne a wata ganawa da aka yi tsakanin Sarki Salman na Saudiyya da Shugaban Gwamnatin Riko ta Sudan, Laftana Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan tare da Firayi Ministansa Abdalla Hamdok, a birnin Riyadh.

Masarautar Saudiyya ta  ce za ta “zuba makudan kudade kan wasu ayyukan zuba jari” da kuma “inganta wasu ayyukan da ake da su yanzu a kasar Sudan,” inji Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Saudiyya.

A nata bangaren Sudan ta yi alkawarin za ta “mara wa Saudiyya baya a tarurrukan kasashen duniya.”