Saudiyya ta ƙaddamar da tallafin wata-wata ga Falasɗinawa
Masarautar Saudiyya ta kuma jaddada aniyarta ta tallafa wa al’ummar Falasɗinawa ta kowace fuska
Ƙasar Saudiyya ta ƙaddamar da shirin ba wa Falasɗinawa tallafin kuɗi a kowane wata sakamakon kashe-kashen da Isara’ila ke musu a yankin Zirin Gaza.
Masarautar Saudiyya ta kuma jaddada aniyarta ta tallafa wa al’ummar Falasɗinawa ta kowace fuska domin rage musu raɗaɗin halin ƙuncin da hare-haren na Isara’ila suka jefa su a ciki.
A ranar Lahadi Saudiyya ta sanar da sabon tallafin kuɗaɗen a matsayin wani ɓangare na ƙara wa al’ummar Falasɗinu ƙwarin gwiwa da nema musu ’yanci.
Wannan kari ne a yayin da tallafin Saudiyya ga al’ummar Falasɗinu ya zarce Dala biliyan 5.3.
- Matashi ɗan Jihar Yobe na gab da ƙwace kambin Gwarzon Ɗaukar Hoto na Duniya
- Harin bom ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin sojoji da al’ummar Kaduna
Masarautar ta jaddada kokarinta wajen tattaunawa da kasashen duniya wajen ganin an daina daukar matakann soji da kuma kare fararen hula gami da isar da kayan agaji ga Falasdinawa.
Ta kara da cewa za ta ci gaba da kokari wajen ganin an kare dukkan hakkokin al’ummar Falasdianwa ta hanyar magance matsalar da kuma tabbatar da ’yancinsu da tabbatuwar Gabashin Birnin Kudus a matsayin babban birnin kasarsu.