Saudiyya ta ɗauki malamai dubu 9 domin koyar da kaɗe-kaɗe a makarantu

A wani yunƙuri mai cike da tarihi da nufin sake fasalin tsarin ilimi a Saudiyya, ƙasar ta ɗauki malamai sama da 9,000 domin fara koyar da ilimin waƙa da kaɗe-kaɗe a makarantun gwamnati a faɗin kasar. Sabon fasalin yana daga cikin gagarumin shirin kawo sauye-sauye ta fuskar al’adu a kasar nan da 2030 (Vision 2030), […]

Saudiyya ta ɗauki malamai dubu 9 domin koyar da kaɗe-kaɗe a makarantu

Yarima mai jiran gadon Masarautar Saudiyya, Muhammad Bin Salman

A wani yunƙuri mai cike da tarihi da nufin sake fasalin tsarin ilimi a Saudiyya, ƙasar ta ɗauki malamai sama da 9,000 domin fara koyar da ilimin waƙa da kaɗe-kaɗe a makarantun gwamnati a faɗin kasar.

Sabon fasalin yana daga cikin gagarumin shirin kawo sauye-sauye ta fuskar al’adu a kasar nan da 2030 (Vision 2030), ƙarƙashin jagorancin Yarima mai Jiran Gado Mohammed bin Salman, wanda ke neman haɓaka tattalin arziki da zamanantar da al’ummar kasar ta hanyar fasahar zamani da nishaɗai da ilimi.

Ɗaukar malaman masu ɗimibin yawa wata manuniya ce ga ƙoƙarin mahukuntan Saudiyyar na faɗaɗa ko buɗe tunani na al’adun matasan kasar, tare da kawar da ɗabi’ar ra’ayin mazan jiya ta fuskar ilimi.

A shekarun baya, ana yi wa koyar da waƙa a makarantu kallon abin ƙyama ko haram, amma yanzu masarautar tana ɗaukaka abin ta hanyar sanya shi cikin manhajar ilimin ƙasar.

Ma’aikatar Raya Al’adu da Ilimi ta Saudiyyar ce ke jagorantar sabon shirin, wanda ya haɗa da kafa sashe ko tsangayar waƙa ta musamman a makarantu.

Malaman, waɗanda galibinsu an horar da su kan wake-wake da kaɗe-kaɗen gargajiya da al’adun kiɗan Larabawa da na zamani, za su koyar da ɗalibai wajen fahimtar kaɗe-kaɗe da waƙoƙi da kayayyakin kiɗan har ma da wasan kwaikwayo.

Jami’ai a Ma’aikatar sun yi na’am da matakin a matsayin wani ci-gaba ga fannin ilimin Saudiyyar.

“Ilimin kiɗa ko waƙa yana da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa fikira da al’ada da natsuwa cikin hankali ga matasanmu.

Haka zalika za ta samar da sababbin damammakin aiki ga matasan Saudiyyar a fannin fasaha da nishaɗi,” in ji wani jami’i.

Kawo ilimin waƙoƙi da kaɗe-kaɗen na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen a Saudiyyar, yayin da masarautar ke ci gaba da sassauta takunkuman da ta sanya a kan harkokin nishaɗi da al’adu.

A ’yan shekarun nan, ƙasar ta buɗe gidajen sinima ta kuma karɓi baƙuncin bukukuwan kaɗe-kaɗe na kasa da kasa, tare da marabtar wasannin kwaikwayo da ’yan wasa na duniya suka yi — abubuwan da ba a yi tsammanin faruwar su ba shekaru goma da suka wuce.

Manufar Vision 2030 na nufin ƙara bunƙasa al’adun Saudiyya, inda harkokin wasanni da fasaha za su taka muhimmiyar rawa wajen rage dogaron da ƙasar take yi da albarktaun man fetur, ta hanyar inganta sababbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga kamar bunƙasa yawon buɗe ido da nishaɗi da al’adu.

Turjiya

Yayin da yunƙurin ya sami karɓuwa sosai daga ƙungiyoyin rajin ci-gaba, a ɗaya gefen yana fuskantar turjiya daga masu ra’ayin mazan jiya waɗanda ke jayayyar cewa ilimin kaɗe-kaɗe na iya gurɓata ko lalata kyawawan ɗabi’u da al’adun gargajiyan kasar.

Amma, gwamnatin ƙasar ta nace kan yunƙurinta, tana mai jaddada cewa ilimin al’adu zai dace ne, maimakon cin karo da tanaden-tanaden addinin Musulunci.

Gabatar da azuzuwan koyar da kiɗan, wani gagarumin sauyi ne inda ɗalibai, waɗanda yawancinsu yanzu ne za su samu damar samun ilimin kaɗeɗe-kaɗeɗe bisa tanadin doka.

Ana sa rai cewa makarantu a faɗin Saudiyya za su fitar da jadawalinsu na koyar da waƙa da kaɗe- kaɗe sannu a hankali, tare da tabbatar da samar da kayan karatu da kayan aiki, sannan ga kwararrun malaman da za su dafa wa sabuwar manhajar.

Yunƙurin da Saudiyya take yi na zamanantar da ilimi ta hanyar fasaha wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa matasanta da kuma shirya su ga tattalin arzikin duniya.

Ilimin kaɗe-kaɗe, wanda a da ana masa kallon bakuwar a’adar da ta samo asali daga waje, yanzu ana rungumar sa a zaman wani ginshikin haɓaka al’adu da gina kasa.

Yayin da Saudiyar take ci gaba da kawo sauyi a karkashin shirinta na Vision 2030, shigar da kaɗe-kaɗe a cikin manhajar ilimin kasar yana nuna wani sabon babi a Masarautar — wanda ta rungumi al’ada da zamani a lokaci guda, yayin da fikira take taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomarta.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta