Saudiyya ta ba Najeriya kyautar tan 50 na dabino

Saudiyya ta ce tallafin na ingantaka ne tsakanin kasashen

Saudiyya ta ba Najeriya kyautar tan 50 na dabino

Dabino

Gwamnatin kasar Saudiyya a ranar Talata ta ba Najeriya kyautar tan 50 na dabino a yunkurinta na inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Alghamdi, ne ya mika dabinon yayin wani biki da aka gudanar a Abuja.

Da yake jawabi a wajen, jagoran kwamitin bayar da tallafin na Saudiyya, Nezat Talaqi, ya ce dabinon kyauta ce daga Saekin kasar, kuma Babban Hadimin Masallatan Harami guda biyu, salman Al-Saud.

Ya ce gwamnatin kasar, ta hannun Hukumar Bayar da Agaji ga Kasashen Waje ta Kasar (KSRelief), ta jima tana bayar da tallafi ga gwamnatin Najeriya ta fuskoki da dama.

Nezat ya ce daga cikin irin shirye-shiryen, akwai tsarin tallafi na Et’am, wanda ya tallafa wa mutum 48,000 da abinci a jihohin kano da Yobe da kuma Borno, wanda ya lashe sama da Dalar Amurka 500,000.

Kaalika, wata sanarwa daga ofishin jakadancin kasar a Najeriya ya ce Cibiyar Jinkai ta Saudiyya na shirin yin gangamin bayar da tallafin lafiya a Abuja da kano da kuma Legas, kuma za a yi ne a watanni uku na biyu cikin shekara ta 2023.

“Bayar da wannan dabinon na cikin irin tallafin da muke bayarwa daga Sarkin Saudiyya, zuwa ga kasashe kawayenmu irin su Najeriya, domin a raba wa mabukata.

Wannan wani yunkuri ne na gwamnatin Saudiyya na kara yaukaka dankon dangantaka tsakanin kasashen biyu a kowanne mataki.

Da yake karbar dabinon, Daraktan Yanki a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Janet Olisa, ya bayyana godiyarsu ga gwamnatin Saudiyya a madadin gwamnati da mutanen Najeriya. (NAN)