Saudiyya ta cafke maniyyata 300,000 marasa takardun aikin hajji

Hukumar ta ce duk mutumin da aka kama ya aikata wannan laifi za ta tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari.

Saudiyya ta cafke maniyyata 300,000 marasa takardun aikin hajji

Mahukunta a ƙasar Saudiyya, sun sanar da kame maniyyata 300,000 waɗanda ba su da takardun shaidar aikin hajjin bana.

A cewar mahukuntan ƙasar, matakin bibiyar waɗanda ba su da shaidar aikin hajjin na da nufin rage cunkoson jama’a, a yayin ibadar wadda kan tattara miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya.

Sanarwar da hukumar kula da cunkoson jama’a ta Saudiyya ta fitar, ta ce cikin mutane har153,998 da suka shiga ƙasar da takardar yawon buɗe ido saɓanin takardar izinin aikin hajji da ya kamata su samu.

Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya, ya ce daga cikin mutanen akwai kuma wasu 171,587 waɗanda suke zaune a ƙasar, amma ba ‘yan asalin ƙasar ba ne, kuma suka fito da nufin aikin hajjin ba tare da takardun izini ba.

Mahukuntan Saudiyya sun yi amannar cewa dubunnan mutane a irin wannan lokaci kan maƙale a ƙasar da bizar Umrah ko kuma ta yawon buɗe ido don gudanar da aikin hajji ba tare da izini ba, wanda kuma shi ke haddasa cunkoson jama’a.

A wannan karon mahukuntan sun sanar da tsaurara dokoki ciki har da zaman gidan yari ga duk wanda suka samu da aikata wannan laifi.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki