Saudiyya ta hana ’yan kasashen waje zuwa Umrah
Saudiyya ta rufe iyakokinta ga harkokin shige da ficen kasa da kasa bayan dawowar COVID-19
Gwamnatin Saudiyya ta dakatar da masu zuwa kasarta domin gudanar da Umrah da ziyara daga kasashen waje.
Ma’aiaktar Harkokin Gidan Saudiyya ta kuma dakatar da zirga-zirgar jirage na kasa da kasa zuwa ciki da kuma fita daga kasarta na tsawon mako guda.
- Mutumin da ya kera kofar Dakin Ka’aba ya rasu
- Sojoji ne suka ceto Daliban Kankara —Fadar Shugaban Kasa
Kazalika ta rufe iyakokinta ga harkokin shige da fice na kan tudu da na teku, wanda ta ce akwai yiwuwar tsawaita wa’adin zuwa mako biyu.
Ma’aikatar wadda ta ce lalura ce kadar za ta iya sa ta bari a shigo kasar, ta wajabta wa duk wanda ya shigo Saudiyya daga kasashen da ke da cutar COVID-19, bisa umarnin Ma’ikatar Lafiya ta Saudiyya, ya killace kansa na mako biyu kafin ya fara fita.
Za kuma a rika yi wa irin wadannan bakin gwajin cutar COVID-19 duk bayan kwana biyar a yayin da suke killace tun daga ranar saukarsa a Saudiyya.
Wani jami’i a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan ya ce nan gaba za a yi wa tsarin gyaran fuska gwargwadon yadda aka tsinci kai a kasar, bisa shawarwarin Ma’aikatar Lafiya ta kasar.