Saudiyya ta damu da yawan matan da ba su yi aure ba

Saudiyya ta damu da yawan qaruwar mata martasa aure, wadanda shekarunsu suka haura 30. Shugaban wata qungiya da ake yi wa laqabi da Wiam, wato Qungiyar kula da rayuwar iyali, Mohammad Al Abdul Qadir, wanda ya bayyana cewa akwai kimanin mata miliyan daya da rabi, wadanda shekarunsu suka haura 30, amma ba su yi aure […]

Saudiyya ta damu da yawan matan da ba su yi aure ba
Saudiyya ta damu da yawan matan da ba su yi aure ba

Saudiyya ta damu da yawan qaruwar mata martasa aure, wadanda shekarunsu suka haura 30. Shugaban wata qungiya da ake yi wa laqabi da Wiam, wato Qungiyar kula da rayuwar iyali, Mohammad Al Abdul Qadir, wanda ya bayyana cewa akwai kimanin mata miliyan daya da rabi, wadanda shekarunsu suka haura 30, amma ba su yi aure ba.

Wannan adadi ya yi nuni da cewa sun kwashi kashe 33.4 cikin 100 na yawan matan da ke masarautar, kamar yadda ya bayyana wa wata jarida da ke fito kullum a qasar Makkah
“Akwai buqatar mu yi tanadi na musamman ga iyalan da ke qasar Saudiyya, wanda za su tafi a kansa na tsawon shekara 10,” inji shi. Domin a cewarsa: “Muna buqatar maganin matsaloli don daidaita rayuwar iyali, ta yadda za nmu shawo kan tuzurancin mata.”
Wata mai fafutikar ’yancin mata a qasa saudiyya, ta ce yawan matan da ba su yi aure ya kai kimanin miliyan biyu.
“Wannan babban al’amari ne mai tsoratarwa, in an yi la’akari da yawansu a tsarin zamantakewar al’umma, lallai akwai buqatar a shawo kan matsalar tun kafin ta haifar da babbar illa,” a cewar mai fafutikar haqqin matan.
Sai dai kuma mafi yawan cin matan ba sa ganin cewa, wannan wata musifa ce ta kunno kai, domin sukan bayyana cewa akwai mata da dama wadanda suka fi sha’awar zama ba tare da sun yi aure ba.
“Akwai wadanda suka qi yin aure, saboda wasu dalilai, sannan akwai wadanda fafutikarsu kawai su gina rayuywarsu,” a cewar ra’ayin wasu.
Jaridar da ta baza labarin, ta bayyana cewa, su kuwa mazan da suka qi yibn aure, sun dora alhakin hakan a kan rashin abin yi da zai ba su damar zama da iyali.
Su kuwa masana zamantakewar al’umma, sun tabbatar da cewa dalilan da ke sanyawa mace ta zauna babu aure sun sha bamban a tsakanin qasashen duniya.
“A Saudiyya, babbar matsalar ita ce wasu zuri’ar kan nemi a ba su sadaki mai dimbin yawa,” a cewarsu, inda suka yi qarin haske da cewa: “Akwai tsadar bukukuwan aure, inda ake kashe maqudan kudi. Irin wadannan matsalolin kan sanya matasa su je, su auro mata ’yan qasashen waje,” inji su.
Duk da cewa mazan da ke zaune a yankin tekun Fasha, sun fi sha’awar auren matan yankinsu, amma dubbai daga cikinbsu suna auren mata ’yan qasashen waje ne.
A shekarar 2010, qasar Kuwait ta kafa kwamitin da zai taqaita auratayya a tsakanin mazan qasar da matan qasashen waje.
A shekarar 2007, wani dan majalisa a qasar Bahraini ya bijiro da buqatar ganin ’yan uwansa maza kan lallai su auri mata hudu, inda za su auri mata uku ’yan qasarsu da daya ’yar qasar waje, ta yadda za a shawo rashin auren mata.
dan majalisa Jasem Al Saidi, wanda ya shafe tsakanin shekarun 2002 zuwa 2014 a majalisar Bahrain, ya jadadda buqatarsa ta ganin mazan sun auri mata fiye da guda saboda sadaukar da kai ga qasarsu.
“Ba ma buqatar mata su zauna babu aure a qasar mu, kuma ba ma buqatar qaruwar yawan sakin aure. Don haka auren mace fiye da daya shi ne amgani, don haka nike shawartar ’yan majalisa da su kasance abin doka misali,” inji shi.
Muhammad AbdulQader, wanda ya bijiro wa al’ummar Saudiyya da wannan matsalar, ya buqaci masana das u bayar da shawarwqarin da ya kamata a aiwtar don kyautata zaman iyali, ta hanyar samar da ayyukan yi da hadin gwiwar iyali a zamantakewar aure, ta yadda gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu za su shigo.
Taron qungiyar kula da rayuwar iyali ta qasar saudiyya, wato Saudi Family Care Societies, wanda za a gudanar a wata mai kamawa, Zai yi nazari kan nau’ukan bincike 30, don tunkarar matsalolin al’umma.