Saudiyya ta fara koro alhazai marasa takardar shaidar aikin Hajji

An fara kame da cin tarar N3.9m ga marasa takardar shiadar aikin Hajji a birnin Makkah, Mina, Arafa, Muzdalifa, cibiyoyin tantance alhazai

Saudiyya ta fara koro alhazai marasa takardar shaidar aikin Hajji

Maniyyatan Najeriya a Saudiyya

Hukumomin kasar Saudiyya sun fara koro maniyyata kan rashin mallakar takardun izinin gudanar da aikin Hajjin 2024.

Ma’aikatar Harkokin Musuluncin kasar ta sanar cewa gwamnatin kasar na kuma cin tarar Naira miliyan 3.9 (Riyal 10,000) ga maniyyata marasa takardar izinin, kan saba dokokin aikin Hajjin.

Sanarwar ta kara da cewa ana kamen marasa takardar izinin aikin Hajji ne a birnin Makkah, Mina, Arafa, Muzdalifa, cibiyoyin tantance alhazai, tashar jirgin kasa, shingayen binciken jami’an tsaro da wasu muhimman wurare.

Ma’aikatar wadda ta ce an raba wa maniyyata katin shaida na NUSUK domin saukaka musu zirga-ziraga, ta kara da cewa za a ci gaba da kamen har zuwa ranar 20 ga watan nan na yuni, 2024.

Ta ci gaba da cewa duk wanda aka kama da laifin safarar maniyyata marasa takardun izinin aikin Hajjin za su fuskanci daurin watanni shida da tarar Naira miliyan 20 (Riyal 50,000), hadi da kwace abin hawansu.

Wadanda ba ’yan Saudiyya ba kuma za a kora su zuwa kasarsu sannan a haramta musu shiga Saudiyya na wani lokaci.

Duk wanda aka kama da laifi fiye da sau daya kuma za a a ninka horon da za a yi musu.

Ma’aikatar ta ce an bullo da tsarin ne domin tabbatar da aminci da tsaron lafiyar alhazai musamman a lokutan ibada a kasar.

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta gargadi alhazanta cewa su a kowane lokaci su kasance dauke da katin shaidarsu na NUSUK domin guje wa kame.

Hukumar ta kara da cewa duk wanda ba shi da katin na NUSUK ba zai samu shiga wasu wurare a kasar ba.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja