Saudiyya ta fara luguden wuta a Yemen

A jiya Alhamis ne kasar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-haren soji a kasar Yemen domin dakile yunkurin ‘yan tawayen Houthi na kwace madafun ikon kasar kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana. Shugaban kasar Yemen ne Abd Rabbuh Mansour ya nemi kasar da ta kawo musu dauki. Rahotanni na nuna cewa ana […]

Saudiyya ta fara luguden wuta a Yemen
Saudiyya ta fara luguden wuta a Yemen

A jiya Alhamis ne kasar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-haren soji a kasar Yemen domin dakile yunkurin ‘yan tawayen Houthi na kwace madafun ikon kasar kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.

Shugaban kasar Yemen ne Abd Rabbuh Mansour ya nemi kasar da ta kawo musu dauki. Rahotanni na nuna cewa ana ta jin hargagin fashewar bama-bamai a filin jirgin sama da wasu sassan Sana’a, babban birnin kasar.
A kwanakin baya ne dai ‘yantawayen suka yi nasarar mamaye kasar ta Yemen, a inda suka sanya Shugaban kasar tserewa fadarsa da ke birnin Sana’a.
Fadar gwamnatin kasar Amurka ta ce Shugaba Barack Obama yana goyon bayan harin da kasar ta Saudiyya ke kaiwa.
Idan dai ba a manta a ranar Juma’ar da ta gabata ne aka kai wasu harin bama-bamai a masallatai biyu lokacin Sallar Juma’a, inda akalla mutane 137 suka rasa rayukansu. Kodayake, masu aiko da rahotanni sun ce masallatan biyu na ‘yan Shi’a ne da ake kira Houthis wadanda suka kwace iko da babban birnin kasar a watan Satumbar bara.