Saudiyya ta hana Shugaban Sudan keta sararin samaniyarta

Hukumomin kasar Saudiyya sun hana jirgin Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir keta sararin samaniyar kasar.Kakakin Shugaban Imad Sayed Ahmed ne ya bayyana haka kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuter ya ruwaito, inda ya ce Shugaba Al-Bashir yana kan hanyarsa ta zuwa Iran ne. Akwai dangantaka mai tsami a tsakanin kasashen Saudiyya da Iran.“A […]

Saudiyya ta hana Shugaban Sudan keta sararin samaniyarta

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na SudanHukumomin kasar Saudiyya sun hana jirgin Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir keta sararin samaniyar kasar.
Kakakin Shugaban Imad Sayed Ahmed ne ya bayyana haka kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuter ya ruwaito, inda ya ce Shugaba Al-Bashir yana kan hanyarsa ta zuwa Iran ne. Akwai dangantaka mai tsami a tsakanin kasashen Saudiyya da Iran.
“A yau hukumomin Saudiyya sun hana jirgin saman Shugaba Bashir ketare sararin samaniyarsu a kan hanyarsa ta zuwa Iran,” inji shi.
Sai dai ba a samu jin ta bakin hukumomin Saudiyya don maida jawabi a kan lamarin ba.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Abbas Arakchi ya ce Iran tana tattara bayanai a kan lamarin. Kuma bai ambaci sunan Saudiyya a matsayin kasar da ta tilasta jirgin Bashir komawa ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Iran (ISNA) ya ruwaito Arakchi yana cewa: “Ofishin Jakadancin Sudan a Tehran ya sanar da mu cewa wata kasa da jirgin Shugaba Omar Al-Bashir zai bi ta cikinta ta ki ba shi izinin keta sararin samaniyarta. Idan gaskiya ne cewa wannan kasa ta dauki wannan mataki, babban abin takaici ne.”
An ruwaito Arakchi yana cewa an nemi izinin ba jirgin Bashir damar keta sararin samaniyar tun kafin ya taso, amma sai aka tilasta masa komawa Khartoum.
Babu wani bayani kan ko Bashir yana kan hanyarsa ta zuwa rantsar da sabon Shugaban Iran Hassan Rouhani, ko kan yadda aka hana jirgin shiga Saudiyya.