Saudiyya ta haramta amfani da sunaye 50 a kasarta

Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida na kasar Saudiyya ta fitar da jerin sunaye 50 da ta hana ’yan kasar amfani da su a wajen rada wa ’ya’yan da za a haifa nan gaba..Kamar yadda sanarwar ta nuna, daga yanzu kasar za ta daina amfani da sunaye irin su Malika da Linda da Amir da […]

Saudiyya ta haramta amfani da sunaye 50 a kasarta
Saudiyya ta haramta amfani da sunaye 50 a kasarta

Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida na kasar Saudiyya ta fitar da jerin sunaye 50 da ta hana ’yan kasar amfani da su a wajen rada wa ’ya’yan da za a haifa nan gaba..
Kamar yadda sanarwar ta nuna, daga yanzu kasar za ta daina amfani da sunaye irin su Malika da Linda da Amir da Sandy da sauransu.
Ma’aikatar kula da harkokin gidan ta kara da cewa ta yi haka ne don ta lura da yawa daga cikin irin wadannan sunaye ba su dace da al’ada d addinin Musulunci da kasar ke bi ba kuma hasalima sunaye ne da ba su da asali a daukacin yankunan kasashen Larabawa. Ma’aikatar ta ce da alama an aro irin wadannan sunaye ne daga sassan duniya musamman Nahiyar Turai.
A ranar Juma’ar da ta wuce ne kafar sadarwa ta Gulf News ta bayyana wannan labari.
Haka kuma daga cikin sunayen da kasar ta dakatar da yin amfani da su sun hada da Linda da Alice da Elaine da kuma Benjamin.
Sanarwar ta ce daga cikin sunayen da aka hana amfani da su akwai wadanda suke alaka da gidan sarauta kamar Amir da ake wa lakabi da Prince a Turance.  Haka kuma Malek ana danganta shi da “Sarki” ko Malika da ake danganta sunan da “Sarauniya”.
Tuni kasar ta kuduri aniyar sanya kafar wando daya da duk wanda ya yi kunnen-uwar shegu da wannan doka wajen rada daya daga cikin sunaye 50 da aka hana amfani da su.