Saudiyya ta kaddamar da gidauniyar tallafa wa Falasdinawa

Yarima Muhammad Bin Salman ya ba da gudunmawar Naira biliyan hudu domin tallafa wa Falasdinawa a Zirin Gaza

Saudiyya ta kaddamar da gidauniyar tallafa wa Falasdinawa

Kayan Tallafin Falasdinawa da kungiyar Zakka Baznas ke shiryawa a birnin Jakarta na Kasar Indonesiya ranar 2, ga Oktoba, 2023. (Hoto: ADEK BERRY / AFP)

Saudiyya ta fara tara kudade da kayan tallafa wa Falasdinawa kwana 25 bayan Isra’ila ta fara ruwan bama-bamai a Zirin Gaza.

Yarima Muhammad bin Salman ya ba da gudummawar Riyal miliyan 20, wato sama da Naira biliyan hudu a ranar Alhamis da aka kaddamar da asusun tallafin Falasdinawan.

Shugaban Cibiyar Jinkai ta Sarki Salman Bin Abdulazeez na Saudiyya, Abdullah al-Rabeeah ya sanar cewa tallafin na daga cikin shirin kasarsa na “taimaka wa Falasdinawa a matsayin ’yan uwan Saudiyya.”

Ma’aikatar Lafiya ta Zirin Gaza da ke karkashin kulawar kungiyar Hamas ta sanar cewa luguen bama-baman Isra’ila ya kashe Falasdinawa kimanin 8,700, wadanda fiye da rabinsu akasarinsu kananan yara da mata fararen hula ne, ta jikkata wasu sama da 15,000.

Hare-haren da Isra’ilar ta kira martani kan harin ranar 7 ga Oktoba da kungiyar Hamas ta kai mata, sun raba Falasdinawa sama da miliyan da gidajensu, kuma a halin yanzu suke matukar neman agaji.

Isra’ila na ci kara shan suka daga kasashen duniya kan abin da suka kira kisan kiyashi da take wa Falasdinawa da ba su ji ba, ba su gani ba a Gaza.

Saudiyya na bugun kirji a matsayin jagorar fafutikar samun ’yantacciyar kasar Falasdinu, kuma ba ta daukar Isra’ila a matsayin halastaciyar kasa.Sabon yakin da Isra’ila ta kaddamar a kan yankin Falasdinawa na Zirin Gaza ya kawo tsaiko ga kokarin Amurka na sasanta Saudiyya da Isra’ila wadanda suka dade a zaman doya da manja.

Saudiyya ta haramta gudanar da gangamin goyon bayan Falasdinawa yadda ake yi a wasu yankin Larabawa da sauran kasashe, lamarin da ya sa ’yan kasar komawa kafofin sada zumunta don bayyana goyon bayansu ga Falasdinu.

A watan Oktoba kungiyar kwallon kafa ta Al Hilal da ke Saudiyya ta wallafa hoton wani dan wasa sanye da mayafin Falasdinawa, amma ba a jima ba ta goge sakon.

Saudiyya na da tsauraran dokokin kan bayyana ra’ayin siyasa har a kafofin sada zumunta.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan