Saudiyya ta maido wa Najeriya kudin abincin alhazai N107m
Kamfanin Mutawwifs ya maido da kudin ne saboda matsalar ciyar da alhazan Najeriya da aka fuskanta yayin Hajjin 2022.
Kasar Saudiyya ta maido wa Najeriya kudi Riyal 542,033 kwatankwacin Naira miliyan 107.8 a matsayin kudin abincin da ba ta samu ciyar da aljazan Najeriya ba yayin Hajjin 2022.
Najeriya ta karbi kudin ne ta hannun Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON).
- MNDPR ta rufe gidan mai da ke sayarwa sama da farashin gwamnati
- Hisbah ta tsare matasa 19 a wajen daurin auren jinsi a Kano
Cikin sanarwar da ta fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Hukumar, Mousa Ubandawaki, NAHCON ta ce kamfanin kula da alhazann Afirka na Mutawwif ne ya bayar da kudin sakamakon rashin ciyar da alhazan kasar yadda ya kamata yayin Hajjin.
Sanarwar ta ce, hakan ya biyo bayan wasikun da NAHCON ta aike wa kamfanin ne na tunatar da shi rashin ingancin tsarin ciyar da alhazan da aka fuskanta a lokacin aikin Hajjin.
Idan dai za a iya tunawa, rahotanni sun nuna yadda alhazan Najeriya suka fuskanci matsalar abinci na wasu kwanaki yayin Hajjin na 2022.
Lamarin da ya sa NAHCON ta rubuta wasikar korafi zuwa ga kamfanin da lamarin ya shafa don daukar matakin da ya ce.
Da yake karin haske game da lamarin, Shugaban NAHCON na Kasa, Zikhrullah Kunle Hassan, ya ce maido da kudin abin a yaba ne.
Ya ce hakan na nuni da yadda hukumar ta zage dantse wajen ganin an gyara kura-kuran da aka yi wa alhazan Najeriya a yayin Hajjin 2022.
Daga nan, ya nuna godiyarsa ga Kamfanin kan maido da kudin da ba su yi aikinsa ba.
Mutawwif kamfanin Saudiyya ne mai kula da sha’anin masauki da abinci da kuma zirga-zirgar alhazan kasashen Afirka a Muna da Arafat a lokacin Hajji.