Saudiyya ta miƙa tayin karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta 2034
Kudirin na zuwa ne kasa da shekara guda bayan Qatar ta karbi baƙuncin Gasar ta Kofin Duniya.
Saudiya ta sanar da matakin mika bukatar neman damar karbar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2034.
Wannan wani mataki ne da ke matsayin yunkurin baya-bayan nan da kasar ta Larabawa ta yi a kokarinta na bunkasa bangaren wasanninta.
- Takardun Karatu: Duk wata hujja da Atiku zai gabatar bakin alƙalami ya riga ya bushe — Tinubu
- An kashe dakaru 100 a kwalejin horas da sojoji a Syria
Hukumar kwallon kafar Saudiya ta sanar da mataki ne kunshe a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.
Yarima Mohammed bn Salman ya ce Saudiyya na fatan shirya Gasar Kofin Duniya mafi kayatarwa daidai lokacin da ta ke sauya fasalin tattalin arziki da bangarorin rayuwar jama’ar kasar ciki har da wasanni.
Kudirin na Saudi Arabia na zuwa ne kasa da shekara guda bayan makwabciyarta Qatar ta karbi baƙuncin Gasar ta Kofin Duniya, wanda ya mayar da Doha kasa ta farko daga yankin Gabas ta Tsakiya da ta karbar baƙuncin gasar a tarihi.
Masu sharhi dai na alakanta sayen Cristiano Ronaldo da kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr ta yi a matsayin abin da ya sake bai wa kasar kwarin gwiwa a kokarinta na karbar baƙuncin Gasar Kofin Duniyar, bayan da ya janyo tarin manyan ‘yan wasa zuwa lig din na Saudiya.
Kudirin Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman da aka yiwa lakabi da Vision 2030 na da nufin garambawul ga fasalin tattalin arzikin kasar don rage dogaro da bangaren man fetur ta hanyar jawo hankalin ‘yan yawon bude ido da zuba jari baya ga bunkasa bangaren wasanni.
Nan da makwanni masu zuwa ne Saudiya za ta karbi baƙuncin wasan karshe na kwallon Golf baya ga wasan damben Anthony Joshua sai kuma wasan karshe na gasar kwallon Tennis na ATP
Haka zalika, a cikin Disamba, Saudiyan za kuma ta karbi baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta kungiyoyi wato Club World Cup, baya ga kasancewarta mai karbar baƙuncin Gasar Kofin kasashen Asiya ta 2027.