Saudiyya ta sako matan Najeriya da ta tsare kan safarar kwayoyi
Saudiyya ta wanke tare da sallamar mata ’yan Najeriya da ta tsare su a lokacin aikin Hajjin 2024 kan zargin safarar hodar iblis
Gwamnatin Kasar Saudiyya ta wanke tare da sako mata ’yan Najeriya uku da ta tsare su a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024 kan zargin safarar miyagun kwayoyi a kasarta.
Saudiyya ta sako matan ne bayan tattaunawar diflomasiyya tsakanin hukumomin kasashen biyu, a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa.
- Mutum 4 sun mutu, bankuna sun ƙone a gobarar tankar mai
- Faɗa da Buratai: Matan ’yan Shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Yadda ma’aikata za su daina jira kafin shigowar albashin watan Janairu
A lokacin aikin Hajjin 2024 ne jami’an tsaron Saudiyya suka kama matan uku Hadiza Abba, Fatima Malah da Fatima Gamboi, da abin da ake zargin hodar Iblis ce, a Filin Jirgi na Yarima Mohammad bin Abdul Azeez da ke Madina.
Babban Jami’in Diflomasiyyan Najeriya a Saudiyya, Ambasada Muazam Nayaya, ya ce, “Kama su na da alaka da wasu ’yan Najeriya biyu da aka kama tun da farko dauke da kwayar hodar Iblis guda 80 da kuma guda 70 .
“An kama matan ne kan zargin hada baki wajen taimakon da safarar miyagun kwayoyi da mutum biyun farkon ke yi.” a cewar ma’aitar, wadda ta bayyana cewa tsare su ya dauki hankali matuka a Saudiyya.
“An sako su ne bayan doguwar tattaunawar diflomsiyya da shari’a da suka kai ga wanke matan daga laif da kuma sallamar su tare da mika su ga Ofishin Jakadancin Najeriya da ke birnin Jidda,” in ji sanarwar.