Saudiyya ta ware Naira biliyan 46.6 don kafa masana’antar shirya fim

Za ta yi amfani da kudaden ne wajen kafa masana’antar a kasar

Saudiyya ta ware Naira biliyan 46.6 don kafa masana’antar shirya fim

Yarima mai jiran gadon Masarautar Saudiyya, Muhammad Bin Salman

Kasar Saudiyya ta ware Dalr Amurka miliyan 100, (kimanin Naira biliyan 46 da miliyan 600) a kokarin da take yi don kafa masana’antar shirya finafinai a kasar.

Bayanin haka ya fito ne daga baki Najla AlNomair, wata babbar jami’a a Hukumar Kula da Raya Al’adu ta kasar, a wajen bikin baje kolin finafinai na duniya da aka yi a Canees da ke kasar Faransa.

A cewar jami’ar, gwamnatin Saudiyyar mai kula da harkokin kasuwanci da tsare-tsare ta ware wannan kudi ne don daukar nauyin harkokin shirya finafinai kama daga kirkira da shiryawa da daukarsa da rarraba shi da kuma tallata shi a kafofin yada labarai.

A wata hirar da daya daga cikin jami’an da hukumar suke aiki tare da jaridar Arab News a bikin, ya ce kasar ta narka wannan kudi ne don ta kawar da matsalar kudi ga masu son shiga harkar finafinai a kasar da hada hannu da samar da wuraren daukarsu da samar da kayan aiki.

Hukumar ta je wajen bikin ne tare da kafa rumfarta ta musamman, don tallata aniyar tata.

Kuma manyan ’yan fim na duniya sun ziyarci rumfar a cewar jaridar ta Arab News.

Tags