Saudiyya ta yi shirin duban watan Sallah
An girke manyan na’urorin hangen nesa domin aikin duban watan Shawwal.
Saudiyya ta kammala shirin duban watan sallah a wannan Alhamis din.
Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Musulmi suka dauki azumi na 29.
- Kungiyoyin da suka kai zagayen kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai
- Mutum 80 sun mutu a turereniyar karbar kayan Sallah
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da mahukunta Masallatan Harami na Makkah da Madina suka fitar a Twitter.
Shafin na Haramain Sharifain ya bayyana cewa daga yau Alhamis za a fara duban watan na Shawwal.
An girke manyan na’urorin hangen nesa domin aikin duban watan Shawwal.
Ana sa ran fara duba watan Shawwal ne a birnin Sudair da misalin karfe 06:09 na yamma, sai garin Tumair inda za a fara duba da 06:22 na dare.
A nan gida Najeriya ma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’umma su fara duban jaririn watan Shawwal daga yau Alhamis 29 ga watan Ramadan.